Related Articles
Garkuwa: Kasancewarka a matsayin shugaban kungiyar masu yabon Manzon Allah a Jihar Kaduna wadanne irin tsare tsare ne ka taho da su a yanzu?
Dogon Baiti : Wannan kungiya ta shu’ara’ul Islam bijahi sayyadil anan, Munzo mun tarar da ita da tsare tsarenta tun daga matakin kasa baki daya, Jihohi da kananan hukumomi da Mazabu baki daya, sai muka ce to ta yaya muna a kaduna zamu kafa shugabannin Mazabu.
Kuma a halin yanzu muna samun nasara kwarai domin a yanzu a kananan hukumomi 16 a Jihar Kaduna babu mazabar da bamu da shugabanci da mambobi da yawa.
Kuma akwai wani tsarin da muke kokarin shiryawa na Koyar da jama’a sana’a saboda muna son duk inda mambobinmu suke kowa ya samu sana’a ya dogara da kansa idan ma yan uwansa zai sa a sana’ar su koya duk mun tanaji komai, sannan kuma da akwai tanaje tanaje da dama duk na ci gaban jama’a.
Sanan kuma akwai wani tsarin yin zama a duk wata da ake haduwa a tattaunawa tsakanin Juna ayi zumunci dukkan kananan hukumomin 16 a hadu a wuri daya in an yi a nan sai kuma wani watan ayi a can domin ayi zumunci, mun kuma kara samun sababbin mambobi da a halin yanzu muna da mambobi a kalla kashi casa’in da biyar a cikin dari.
Garkuwa : Yanzu Mambobin mutum nawa ne?
Dogon Baiti : A yanzu haka muna da mambobi dubu daya da dari uku (1300) wadanda suka yi rajista, akwai kuma wadanda ba su yi rajista ba sun kai dari Bakwai ( 700) wanda kaga idan suka yi rajista muna da mambobi sama da dubu biyu kenan masu rajista.
Garkuwa : Kayi maganar matakin mazabu ko kuna da tunanin yin siyasa ne?
Dogon Baiti : A gaskiya muna da wannan tunanin domin ko ita uwar kungiyar ta kasa ta bude wani bangare na harkokin siyasa domin a samu bunkasa harkar yabon Annabi Sallahu Alaihi wasallam (SAW) saboda muna samun tsaiko game da gudanar da wadansu al’amura musamman a kan irin yadda ya dace a taimaki harkar.
Sai muka ga ya dace muna mu shiga a yi damu tun da dai Wasunmu nada ilimin da za su iya yin wannan harka ta siyasa.
Misali kamar a Jihar Kano akwai sha’irai da suke a yanzu yan majalisar Jiha ne kuma akwai shugabannin kananan hukumomi da kansiloli duk a halin yanzu.
Kuma idan ka yi misali da ni kaina a nan Jihar kaduna na yi takara kuma cikinnikon Allah ni na zo na uku a matakin da na yi takara, muna son bunkasa harkar har Allah ya Kaita duk inda bamu yi tsammani ba.
Akwai kalubale a tattare da batun Koyar da sana’a, shin ko akwai wata hanya ta samun kudin shiga domin harkar?
Dogon Baiti : To da farko dai a nan Jihar Kaduna duk wani sha’iri zaka ga yana da sana’arsa ko wani aikin da yake yi saboda wasu ma zaka ga ma’aikatan Gwamnati ne, kamar ni nan dan kasuwa ne sosai kuma ni ma’aikacin wadansu kamfanoni ne masu harkar kayan masarufi na yau da kullum don haka tun asali kowa yana da sana’arsa a cikinmu.
Kuma sai muka dauko wani tsarin kaiwa ga wadansu domin su samu sana’a saboda haka ne muka yi tsarin bude makarantun koyon sana’o’i wanda a yanzu haka muna kan tsarin.
Mu Kaita kowace karamar hukuma ta yadda dukkan mambobi za su koyi sana’a kowa ya samu ya dogara da kansa a cikinnmambobin kungiyar shu’ara’ul Islam har ma da wadanda ba mambobin ba su shigo su koyi sana’a.
Garkuwa : Akwai wadansu yan siyasar da suka taba jawo ku domin ku yi tafiya tare da su?
Dogon Baiti : To ita dai wannan kungiyar shekaru 20 kenan da kafuwa a Kaduna, kuma kasancewar kowa ce kungiya nada damar yin musharaka da kowa har da Gwamnati.
Kuma tun zamanin Makarfi muka yi tabi domin shi Makarfi ya san mu mun san shi har zamanin Namadi Sambo duk sun san mu amma dai ba wanda ya taka wata rawar azo a gani sai lokacin Yakowa ya rika bamu wani kaso kuma bamu kadai bane ake yi wa hakan a lokacin, haka da zuwan Muktar Ramalan Yero shima ya Dora daga inda Yakowa ke ba jama’a har zuwa wannan Gwamnatin sai aka Dakatar da na kowa ba namu kadai ba, don haka babu wani tallafin da muke samu a Gwamnatance haka
Sai dai a can baya wadansu shugabannin kananan hukumomin davsuka gabata a baya sun rika Tallafawa wannannkungiya a lokacin Maulidi, amma dai a yanzu babu wani tallafin da muke samu.
Garkuwa: Abubuwa na tafiyar da kungiya basa rasa kalubale shin ko akwai kalubalen da kuke samu?
Dogon Baiti : Hakika muna da kalubale a cikin kungiya da kuma wajenta, a cikin kungiya shi ne ana son dukkan sha’iri zai fadi Annabi (SAW) ya san waye shi in zai yi baitin wake me zai fada kuma ya san abin da zai fadi, amma ana samun wadansu da ba a cikinmu suke ba sai suje suna ta sakin Baki suna fadin abin da ba daidai ba kuma mutanen gari na ganin tare suke da mu alhalin ba tare suke damu ba.
Mu a tsarin mu duk wanda ya yi waka sai ya kawo an duba ta domin a cire duk wani abu kuskure, kuma masu yin gyaran nan Malamai ne Shehun nai su duba domin a gyara komai idan akwai wata matsala ko kuskure a cikin wakar, aji tsantsar waka babu wani abu a ciki da za a ce ba haka ba, to, wannan kalubale ne da muke ta kokarin gyara shi a cikin jama’atu shu’ara’ul Islam.
Sai kuma kalubale ga wasu da suka kasa fahimtar irin gudunmawar da wannan tafiyar take bayarwa, wanda danka ne idan ka aike shi sai kaji yana ta wake wake wata wakar ma zaka ji batsa ce amma a yanzu mun kawo canji gagarumi a cikin jama’a, inda a yanzu hatta da Wayoyin jama’a da an kirasu sai kaji zikiri ne ko yabon manzon Allah ne kuma wannan cikin jama’a kashi tamanin haka suke a yanzu duk wannan gagarumin canji ne aka samu kuma muna ganin tasirin haka.
Kuma akwai Hadisin annabi da ke cewa ku Ladaftar da yayanku abubuwa uku wato son Manzon Allah, son ahalin gidansa da son karatun alkur’ani to shi ne muke ta kokarin mu cusawa yara amma kalubalenmu shi ne iyaye da wasu daga cikin jama’a har yanzu ba su fahimce mu ba.
Garkuwa: Wane kira kake wa yayan kungiya?
Dogon Baiti : kiran da nake yi wa yayan Kungiya shi ne su kara Daura dammara wannan al’amari da muke yi Allah ne kawai yake biyan mu ba wani dan adam ba, kamar yadda yake Allah ne ke bayar da rabo annabi ne ke rabawa to daga ciki a wannan harkar wani kaga ya samu mota, kujerar Umara ko aikin Hajji da sauransu amma ba wai mamban mu ya dogara da hakan bane kowa nada abin da yake yi mun dauki yabon annabi Ibada ne don haka mu kara tsaftace harkar mu sa ikilasi mu yi domin Allah kuma mu koma makaranta saboda shi ilimi ba a karewa mu koma makaranta mu samu ilimin sanin annabi ta yadda zamu Fade shi sosai.
Garkuwa: Kana da wani kira da zaka yi wa Gwamnati?
Dogon Baiti : kira na ga Gwamnati shi ne ta fahimci muhimmancin mu a cikin al’umma domin muna da muhimmanci kwarai.
Akwai lokacin da a wannan Jjhar aka yi ta samun tashin hankali da fitina sai da Gwamnati ta rika yin amfani da sha’irai suna ta yin Wakokin shin yaya annabi yake kuma yaya annabi Isa yake kuma har yanzu akwai wasu daga cikin malaman Kiristoci suna amfani da irin wannan baituka na wakokin zaman lafiya saboda tasirin su.
Ina kira ga Gwamnati da ta san tasirin mu a cikin al’umma domin mu masu kokarin fadakar da jama’a ne yaya annabi yake domin shi yana Koyar da zaman lafiya ne da ci gaba da zaman lumana.
Garkuwa : Na gode
Dogon Baiti: Muma mun gode