Home / Kasashen Waje / MATA KU ZABI JAM’IYYAR PNDS TARAYYA – DOKTA AMINATOU

MATA KU ZABI JAM’IYYAR PNDS TARAYYA – DOKTA AMINATOU

Daga Imrana Abdullahi

An yi kira ga daukacin mata al’ummar Nijar mazauna Najeriya da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin su zabi jam’iyyar PNDS tarayya a zaben dan majalisar Nijar da ke zaune a wajen kasar

Kamar dai yadda aka Sani a nan ba da jimawa ba ne za a yi zaben dan majalisar Nijar da mazauna Najeriya za su yi zabe, kamar yadda dokar kasar ta tanada.

Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad ta bayyana a wurin gangamin da aka yi a birnin Kebbi hedikwatar Jihar Kebbi a arewacin tarayyar Najeriya.

Hajiya Aminatou Abdoulkarim Muhammad ta ce kamar yadda aka Sani mata sun yi rajistar Jefa kuri’a har sama da dubu (13000) lokacin da aka yi wa jama’a rajista, a saboda haka  Mata ku fito kwanku da kwarkwatarku domin zaben jam’iyyar PNDS tarayya.

“Ina yin kira ga daukacin al’ummar Nijar mazaunan Najeriya da kowa ya farka ya Sani cewa jam’iyyar PNDS ce ta cancanta a zaba a ranar zabe saboda ita ce mai kudirin inganta rayuwar dukkan yan Nijar da ke zaune a Nijeriya”.

Aminatou ta kara da cewa babu Buzu ko Bafillatani, Bazabarme, Ba tube babu dai kowace kabila in ba Nijar ba don haka ayi gangami a zabi PNDS tarayya.

Hajiya Aminatou Andoulkarim Muhammad, ta kuma yi kira ga daukacin mata da su himmatu kamar yadda aka san su cewa kuri’a na wurinsu to, kada su yi sakaci kowa ya tashi tsaye a tabbatar an ba jam’iyyar PNDS tarayya kuri’ar da ya dace.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.