Home / Big News / Mata Na Bukatar Ayi Masu Adalci – Honarabul Halima

Mata Na Bukatar Ayi Masu Adalci – Honarabul Halima

Daga Imrana Abdullahi
Honarabul Hajiya Halima Zubairu Danbatta,ta yi kira ga daukacin mahukunta da dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin gudanarwa a kasa da su duba samun karin tallafawa mata a kowane irin mataki da ake tafiyar da Najeriya.
Honarabul Halima ta ce hakika mata suna gwagwarmaya kala kala a rayuwa da yawa don haka a yi masu adalci a kowane fanni.
Honarabul Halima Zubairu ta bayyana hakan ne a wajen wani babban taron da aka shirya wa mata domin fadakar da su a game da wadansu al’amuran da suke tattare da su na rayuwa taron dai an yi shi ne a Kaduna.
“Muna bukatar ayi wa mata adalci ne don haka muke bukatar ayi mana hakan ba wai muna son a ayi dai dai to ba ne, kawai abin da muke bukata dai shi ne adalci ta yadda za a rika jin koke koken mata ta yadda za a samu a ƙalla koda rabin matsalolin mata ne a warware su.
“Ta yaya idan aka duba a majalisar dattawa ta kasa amma ace wai kawai mata guda hudu ne kawai a majalisar cikin yan majalisar dattawa sama da dari, ai wannan abin a duba ne ta yaya za a samu dai daitawar al’amuran ai ba zai yuwu ba.saboda haka ne muke yin kira ga iyayen mu, yan uwa,kakanni,ya’yan mu da su ba mu dama suma mata su shiga cikin wani bangare na harkar mulkin kasa”, inji honarabul.
Sai kuma ta yi kira ga iyaye ba wai yaya ba kasancewar ba wani yaro ko yarinyar da zai matsa wa kansa yin auren wuri don haka nake yin kira ga iyaye da su fahimci cewa a yanzu akwai ilimi ya yi yawa kuma fadakarwa da fahimta duk sun yi yawa don haka mata na bukatar a ilmantar da su ta yadda za a karfafa masu saboda a halin yanzu akwai matsalar mace – macen aure a yanzu ko saki – a nan da – can koma batun tabin hankali na mata a cikin harkar aure don haka a karfafa wa mace ta yadda za ta iya inganta kanta a cikin rayuwar auren. Don haka nake yin kira ga iyaye da su kara karfafa wa ƴaƴansu ta fuskar ilimi ba wai yin auren dole ba”.
Sai ta ce akwai wata matsalar da ke samuwa a rayuwar dan Adam ta jin zafi ko bacin rai da mutum zai iya dandanawa ta fuskoki da yawa, musamman Ni na ta ba samun matsalar mutuwar dan da na haifa, don haka wani al’amari ne na kaddarar da mutum zai iya samun kansa a ciki don haka sai mutum ya rungume ta wato idan irin wannan kaddarar ta same shi saura kuma sai a barwa Allah.

About andiya

Check Also

SAKON ALHERI NA RAMADAN

  Daga Mai Girma, Jakada Dr. Malami Shehu Ma’aji (MFR) Shugaban, Kwamitin Shawara, Hukumar Kare …

Leave a Reply

Your email address will not be published.