Home / Labarai / Matsalar Tsaro Ta fi Yi  wa Arewa Illa Bisa Ga Cutar Korona – Bafarawa

Matsalar Tsaro Ta fi Yi  wa Arewa Illa Bisa Ga Cutar Korona – Bafarawa

Matsalar Tsaro Ta fi Yi  wa Arewa Illa Bisa Ga Cutar Korona – Bafarawa

 

Mustapha Imrana Abdullahi
Tsohon gwamnan jahar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya baiyana cewar, babba matsalar dake addabar yan arewa a halin yanzu kuma take kara barazana ga rayukansu babu kamar matsalar tsaro wadda taki ci taki cinyewa fiye da cutar numfashi ta COVID-19.
Bafarawa ya fadi haka a taron da yayi da yan jarida dangane da yanayin da kasa take ciki a garin Abuja da maraicen yau Larba.
Ya baiyana cewar, baya ga matsalar tsaro akwai ta yunwa da rashin aikin yi da suka yi katutu a kusan kowane lungu na yankin arewa,matsalar da ta wuce cutar Korona birus ko COVID-19 a turance.
” Babba jarabawa da matsalar mu a arewa bata wuce rashin tsaro ba, abin da ya janyo anyi hasarar rayuka da dukiya mai dimbin yawa; kuma har yanzu yankunanmu na jihohin Sokoto, Zamfara da Niger da Katsina da Borno ana kai hare-hare na ta’addanci, satar jama’a da sace dabbobi fiye da wannan matsalar ta cutar numfashi” inji Bafarawa.
Dangane da haka ya nemi a sake lale akan hanyoyin da ake binna zuba makudan kudaden tare da batar dasu da sunan yaki da cutar Coronavirus don mayar da hankali ga baiwa jami’an tsaro issasun kayan aiki da taimako ga wadanda suka shiga cikin wannan bala’i.
Ya nemi gwamnatin tarayya da ta hamzarta baiwa sha’anin tsaro muhimmanci da sanya muhimman matakai ga ganin an kawo karshen kisan al’umma da yi musu barazana fiye da irin yadda ta dauki mataki akan lamarin yaki da cutar.
Bafarawa ya baiyana an batar da naira biliyan 3.5 ba tare da muhimmin bayani akan yaki da cutar amma anyi watsi da matsalar tsaro an koma ma cuter dake dauki daya daya.
Haka ma ya nuna dacewa da yiwa al’ummar kasarnan bayani akan hanyoyin da ake bi akan kashe makudan kudaden yaki da cutar da fitowa da hanyoyin ilmantarwa akan alluran cutar da yadda za ayi maganinta.
Daga karshe ya baiwa shugaban.kasa Muhammadu Buhari shawara da ya mayar da hankali ga kara daukar matakai masu tsauri don yaki da ta’addanci da Boko Haram tare da sanya shugabanin addini, tsofffafin jami’an tsaro da yan siyasa dake da kusanci da jama’a don kara karfin guiwa ga samun nasara akan wannan lamari.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.