Home / KUNGIYOYI / Matsayar Kungiyar Matasan Kiristoci Game Da Takarar Bola Tinubu Da Kashim Shetima

Matsayar Kungiyar Matasan Kiristoci Game Da Takarar Bola Tinubu Da Kashim Shetima

Matsayin Kungiyar Kwararrun Matasan Kiristicin Arewacin Najeriya (NCYP) Game Da Batun Daukar Musulmi Da Bola Ahmed Tinubu Ya Yi Matsayin Mataimakinsa
Bayan da Bola Tinubu ya samu nasarar lashe zaben fitar da Gwani a jam’iyyar APC a watan Yuni na wannan shekarar, yayan wannan kungiya ta NCYP sun yi ta addu’o’i , suna ta tuntuba da ban baki da kuma jawo hankulan jama’a tare da fadakarwa a samu hadin dan takara da mataimakinsa Musulmi da Kirista, tsarin da muke ganin shi ne zai zama an yi dai- daito na gaskiya da adalci, musamman a wajen gudanar da mulkin Najeriya. Amma abin da muke nufi bai samu ba.
Muna sane da cewa ka na neman murya kamar ta irin shugabancin NCYP saboda haka “To a halin yanzu da yake Bola Ahmes Tinubu ya zabi musulmi a matsayin mataimakinsa, ina ne matsayar mu? Za mu goyi bayan wata jam’iyya ne? Ko kuma har yau muna tare da Bola Tinubu?.
Wadannan su ne tambayoyin
Saboda haka ne a yau muka yanke shawarar mu gaya maku cewa har yanzu muna tare da Bola Ahmed Tinubu da kuma Kashim Shetima saboda mun yi imanin za su iya magance matsalar tsaron da ke samun mu.
Saboda haka a matsayin mu na matasa, Bola Tinubu da Kashim Shetima duk sun yi amfani da kokarin daukar matasa aiki domin rage matsalar tsaro da kuka kokarin bunkasa tattalin arzikin kasa ta yadda rayuwar jama’a ta inganta.
A Jihar Legas, yadda Tinubu ya aiwatar da gagarumin aikin daukar matasa aiki da aka fi Sani da agberos a hukumar kula da dokokin tuki, da hukumar kula da tsaftace muhalli da dai sauransu da dama, wannan ya rage matsalar aikata laifuka da ya haifar wa Jihar samun zaman lafiya da bunkasar kasuwanci da ya taimakawa Jihar na tsawon lokaci. Wannan shi ne sirrin da ke cikin bunkasar da Jihar Legas Legas samu musamman wajen tattara kudin shiga.
Kashin Shetima a shekarar 2012 ya samu nasarar tseratar da garin Maiduguri babban birnin Jihar Borno daga hannun yan ta’addan Boko Haram. Lokacin da ya samawa matasa dubu Ashirin aiki a cikin rundunar yan kungiyar sa kai, wannan ya taimaka kwarai wajen fitar da Boko Haram daga birnin Maiduguri.
Wadansu masana harkokin tsaro sin tabbatar da cewa idan bam da kokarin da Kashim ya yi na daukar matasan aikin tsaro da babban birnin ya fada a hannun yan Boko Haram kuma hakan zai iya ba su damar mamaye dukkan yankin Arewa maso Gabas, wanda hakan zai zamar wa Najeriya da yankin nahiyar Afrika musamman kasashen kungiyar rainon Ingila ECOWAS cikin mummunan garari.
Babu wata shakka ko tantama a cikin zuciyar mu cewa da Bola Tinubu da Kashim za a samu dimbin matasan da za su samu aikin yi ba a arewacin Najeriya kadai ba har da baki dayan kasa.
Tuni had mun fara tattaunawa game da batun bude masakun da ke arewacin Najeriya musamman na wanda ke Jihar mu ta Kaduna. Da za a iya samawa matasa a kalla dubu dari Balwai (700,000) aikin yi idan aka bude masana’antun. Da akwai wadansu masana’antu kamar hakan a Jihar Kano da kuma wasu Jihohi da yawa a arewacin kasar da za a bude su. Wannan ne matakin farko da za a samu yin maganin matsalar tsaro musamman na yan Boko haram da kuma yan bindiga.
Ga wani misalin kuma shi ne irin yadda Tinubu ya kasance mutumin da ke tsananin nuna kauna da Soyayya ga Kiristoci, matarsa babbar Fasto ce a Cocin Redeemed Christian Church Of God; shi ne kuma Gwamna na farko da ya dauki makarantun mishau ya mayar masu, wadanda aka mikawa Gwamnati a zamanin mulkin sojiji. Tinubu ya mayarwa da Coci Coci da makarantun da nufin a samu karin inganta harkokin ilimi a Jihar Legas. Hakika irin wadannan matakan da jawaban ya dauka sun haifar da nasara sai kuma irin yadda ya rika bayar da wurare ga Coci Coci da yawa a Jihar Legas.
Dangantakar Kashim Shetima da Kiristoci a baki dayan rayuwarsa hakika mai Armashi ne, abokansa da suka yi a wuraren aiki daban daban duk sun tabbatar da hakan. Kuma al’ummar Kiristocin Jihar Borno suma sun bayyana hakan ta fuskar gina Coci Coci da yan Boko haram suka lalata musamman wadanda ke a Kudancin Jihar Borno Kiristocin sun kuma samu kujerun zuwa ziyarar aikin hajji na Kiristoci duk wanda Gwamnatin da ya yi wa jagoranci ta dauki nauyi, wannan na nan a cikin zukatan al’ummar mu.
Ya ku yan uwana ya dace mu ajiye duk wata jita jita a gefe, my tambayi kawunan mu wadansu tambayoyi masu muhimmanci.
Shin Tinubu da Shetima na da kwarin Gwiwar samun nasara a kan duk wani dan takara har su samu nasara a zaben 2023 mai zuwa? Wannan haka ne ba wata tantama.
Saboda haka baku tunanin cewa abu ne mai muhimmanci muyi aiki da hankali mu yi aiki tare da su da suke da kwarewar warware matsaloli kuma suke da karfin Gwiaar lashe zaben shugaban kasa da mataimakinsa na tarayyar Najeriya?
Idan a matsayin mu na al’ummar Kiristocin da ke arewacin Najeriya ba mu yi duba na musamman kuma tsanani ba muka fahimci wadansu matsalolin da zamu bayar da hadinnkai da goyon baya wajen aiki warware su ba, to zai yi wahala mu samu canjin da muke bukata. Mu daina Dora laifi a wani wuri can daban mu dai yi aiki wajen warware matsalolin kawai.
Akwai abubuwa da dama da ya dace mu samawa al’ummar mu domin taimakawa kawunan mu. Dole sai mun sadaukar. Sai mun yi aiki tukuru domin samun abin da ya dace mai girma fiye da kowane dayan mu. Wannan ne ya sa kungiyar NCYP suka yanke hukunci na daukar matsayin da zai iya zama kamar wani abu daban a gare ku. Ko ba komai mun dauki mataki kuma muna kokarin yin aiki sosai.
Kwarai babbar tambayar da za mu yi shi ne yaya zamu samu ci gaba?
Dole me kungiyar NCYP ta bayyana cewa ba wai muna da jadawalin yadda za a gudanar da komai ba dari bisa dari a kan haka. Amma abin da muke bayar da tabbaci shi ne zamu bincika sai mun gano dukkan matsalolin da al’ummar Kiristoci ke fama da su.
Saboda haka mun shirya bi kofa kofa gida gida domin fadakar da jama’a game da bukatar da ke akwai na a bayar da hadin kai da goyon baya ga Bola Ahmed Tinubu. Har sai mun samu nasarar warware dukkan matsalolin da ke addabar mutanen mu.Kuma.za.mu tabbatar da cewa wadannan kudirin na cikin abin da Gwamnatin da Bola Ahmed Tinubu zai jagoranta, don haka Kiristocin arewa ya dace su bashi hadin kai da goyon baya, a kuma zabe shi a lokacin zaben shekarar 2023.
Ya ku jama’a Maza da Mata, muna kyautata zaton kun fahimci muhimmancin wannan.
Shin muna iya yin hakan?
Kwarai, muna yi. Bari mu gaya maka dalili. Lokacin da injiniyan da ya fi kowa ne ke kokarin mayar da hankali a kan kudirin da zai yi aiki a kai na tsawon shekaru, Noah da iyalai suka kera Jirgi. Kuma wannan Jirgin ya tserar da nau’o’in dabbobin da Allah ya halitta.
Wannan shi ne labarin da duk wani Kirista Kirista Sani. Kuma labarin wata matashiya ce da Allah ya baka da kuma karfin Gwiwar samar da kariya ga jama’a.
Shin had yanzu kuna da wata tambaya? Idan ka na da ita, ba zamu gajiya ba. Sai dai, muna son gaya maka cewa kungiyar NCYP da duk wani rukunin Kiristoci, da kuma Musulmi da ke son yin wata tankiya saboda Kiristoci a Arewa.
Kai ne amsar tambayar da zaka tambaya. Don haka ka dauki matakin aiwatar wa a yau. Domin idan ba mu yi abin  da ya dace ba, to wa zai yi mana?
Wannan kungiya ta matasan Kiristocin arewacin Najeriya sun yi zabe na bayar da hadin kai da goyon baya ga Bola Ahmed Tinubu da duk masu yi masa fafutukar samun nasarar lashe zabe domin samawa Kiristocin arewacin Najeriya mafita tare da daukaka.
Muna yin kira ga duk wani Kirista a arewacin Najeriya da ha himmatu wajen kokarin aiwatar da aiki tukuru domin samun ci gaban da kowa ke bukata.
Saboda haka muke gayyatar duk wanda ya yi imani da wannan da ya zo ya hada hannu da kungiyar kwararrun matasa ta NCYP domin fafutukar samun ingantacciyar alkibla a matsayin mu na Kiristocin arewacin Najeriya mu bayar da goyon baya da duk wani hadin kai ga Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shetima.
FASSARA IMRANA ABDULLAHI

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.