DAGA IMRANA ABDULLAHI
Kogunan Gusau Muktar Shehu Idris ya bayyana wa manema labarai cewa ko tantama babu su ne za su lashe zabe domin jama’a su suke so kuma su suke zabe a koda yaushe.
Muktar Shehu Idris ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin Gusau hedikwatar Jihar Zamfara.
Muktar Shehu Idris ya ci gaba da yin kira ga daukacin al’umma da su kara ninka goyon baya da hadin kan da suke ba jam’iyyar APC domin kwalliya ta biya kudin Sabulu.
“Muna sane da cewa jama’a na son mu kuma mu za su zaba don haka nasara a gare mu take a koda yaushe cikin yardar Allah madaukakin Sarki”.