Imrana Abdullahi
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya yi kira ga daukacin yan Nijeriya da su daina zama su na lisaafin abin da Sa Ahmadu Bello Sardauana ya aikata a lokacin rayuwarsa.
Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana hakan ne a wajen babban taron shekara shekara domin yin laccar tunawa da marigayi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato daaka yi a dakin taro na cibiyar.
Malam Shekarau ya ci gaba da cewa hakika lokaci ya yi da jama’a za su daina yin taro su na lissafa irin abin da Sardauna ya aikata na ciyar da Arewa da kasa gaba baki daya.
“Idan muka yi duba da kyau za mu ga cewa mu dukka jagororin da suke da rai a halin yanzu duk mun wuce shekaru shittin a duniya don haka kowa ya rika tunanin gudunmawar da zai bayar wajen ci gaban kasa, saboda marigayi Sardauna duk abin da ya yi za a ga ya na matashi ne domin ya rasu ne ya na da shekaru 55 a duniya saboda za ku ga cewa ya bayar da gudunmawar da ake takama da ita ne tun ya na da shekaru Talatin da wani abu, amma kullum ana kiran sunansa shi ya yi kaza da kaza”, inji shekarau.
Saboda haka muna kira ga daukacin matasa da su fara tunanin bayar da gudunmawarsa kamar kowa domin ta haka ne kasa za ta ci gaba.