Home / Big News / MUHAMMAD SANI DATTIJO YA KADDAMAR DA TAKARARSA A KADUNA

MUHAMMAD SANI DATTIJO YA KADDAMAR DA TAKARARSA A KADUNA

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
A wani gangamin taron magoya baya kwamishinan ma’aikatar kasafin kudi da tsare tsare na Jihar Kaduna Mohammad Sani Abdullahi Dattijo ya kaddamar da takararsa domin neman APC ta tsayar da shi Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar.
A wajen babban taron da ya jagoranci gangamin magoya bayansa a sakatariyar jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna Sani Dattijo wanda ya kasance tsohon shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin Jihar Kaduna  ya tabbatarwa da dimbin magoya bayansa da kuma shugabannin APC cewa idan an bashi jagorancin Jihar Kaduna ba za a ji kunya ba, domin kamar yadda ya tabbatar kwalliya za ta biya kudin sabulu.
Sani Dattijo, ya ci gaba da bayanin cewa kasancewarsa mutum mai kishi domin san ganin Jihar Kaduna ta tserewa tsara ya sa a koda yaushe yake kwana da tashi a kan lalubo hanyoyin ciyar da Jihar gaba.
A bayanin da muka samu a wajen wani taron manema labarai da ya gudana a Otal din Asaa pyramid cikin garin Kaduna da aka gayyaci wadansu yan jaridu yan kalilan an ruwaito dan takarar da ke neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Sani Abdullahi Dattijo,na cewa ya tsara jadawalin wadansu Kudirori guda shida da in an zabe shi Gwamnan Kaduna zai aiwatar da nufin ciyar da jiha da kuma al’ummarta gaba.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.