Home / News / BANCE WANI YANKI BA ZAI IYA CIN ZABEN SHUGABAN KASA BA – TAMBUWAL

BANCE WANI YANKI BA ZAI IYA CIN ZABEN SHUGABAN KASA BA – TAMBUWAL

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya Karyata wani rahoton da ake danganta wa da shi cewa wai wani yanki ba zai iya cin zaben shugaban kasa ba idan jam’iyyar PDP ta tsayar da dan takara daga yankin.

A cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun mai ba shi shawara a kan harkokin yada labarai Muhammad Bello da aka rabawa manema labarai cewa hakika wannan rahoton ba gaskiya ba ne, an dai shirya shi ne kawai domin a karkatar da hankulan jama’a kawai.

 

Ga dai bayanin kamar hada; ” An jawo hankalin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya zuwa wani kanun labari na batanci a wani labarin da wata jarida ta rubuta, da yake cewa wani yanki a cikin kasar nan ba zai iya cin zaben shugaban kasa ba”.

About andiya

Check Also

Ramadan 2023: Nigerian Church Reaches Out To Over 1000 Underprivileged Muslims/ Almajiri.

  The church of Christ Evangelical and life Intercessory Ministry, Sabon Tasha Kaduna State has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.