Home / News / MUN GAMSU DA JAGORANCIN GWAMNA MATAWALLE – YAN JIHAR ZAMFARA

MUN GAMSU DA JAGORANCIN GWAMNA MATAWALLE – YAN JIHAR ZAMFARA

Daga Imrana Abdullahi

 

Sakamakon irin kokari da aiki tukurun da Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Muhammad Bello Matawalle, ke yi wajen ganin al’ummar Jihar sun samu ci gaba ta fuskar cin ribar Dimokuradiyya ya sa yan asalin Jihar mazauna garin Auchi suka sauka a babban birnin tarayyar Abuja domin yin godiya da kuma nuna ana tare ga Gwamnatin Muhammad Bello Matawalle.

Mai bayar da shawara ga Gwamnan Jihar Zamfara a kan hulda da kasashen waje da kuma kungiyoyi Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ne ya tarbi tawagar a babban birnin tarayya Abuja kan hanyarsu ta zuwa Shinkafi.

Kamar yadda Jagororin tawagar suka shaidawa mai ba Gwamnan Jihar Zamfara shawara da tawagarsa cewa suna tare da Gwamna Muhammad Bello Matawalle da kuma Gwamnatin da yake yi wa jagoranci dari bisa dari, hakan ya sa duk da muna kan hanyar zuwa Shinkafi daga garin Auchi, mun amince da yada Zango a nan garin Abuja ne domin jaddada mubaya’armu ga Gwamna tare da Gwamnatinsa baki daya.

“Kuma muna yin hakan ne saboda muna yin haka ne da nufin bayar da gudunmawa ne da nufin a samu kwalliya ta ci gaba da biyan kudin Sabulu”.

Sun tabbatar wa da duniya cewa ” Gwamna Muhammad Bello Matawalle mutum ne mai kishin Jihar Zamfara, don haka bayar da cikakken hadin kai da goyon baya a gare shi abu ne da ya zama wajibi, musamman a gare mu da dukkan wanda ke a karkashin mu”.

Sakamakon hakan ne suka ce sun lashi Takobin tashi tsaye domin fadakarwa ga jama’a wajibcin da ke kansu na himmatuwa shiga sako da lungu na Jihar Zamfara domin fadakar da al’umma su zabi Gwamna Matawalle, APC da dukkan yan takarar da suka tsaya neman a zabe su domin darewa kan madafun iko musamman a majalisun Jiha da na tarayya baki daya.

Sai tawagar al’ummar Zamfara mazauna Auchi suka ci gaba da tafiya zuwa Jihar Zamfara musamman ma garin Shinkafi.

 

Da yake mayar da jawabi Mai ba Gwamnan Jihar Zamfara shawara a kan hulda da kasashen waje Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, alkawari ya yi wa tawagar na sama masu da kayan da za su yi amfani da su domin shiga sako da lungu na duk fadin Jihar Zamfara domin yada manufar Gwamna Matawalle da Gwamnatin da yake yi wa jagoranci.

Kuma tawaga karkashin Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ta ci gaba da shirye shiryen tafiya zuwa garin Auchi Jihar Edo,Legas, da sauran wadansu Jihohi domin fadakar da yan asalin Jihar Zamfara muhimmancin komawa gida domin kada kuri’unsu a lokacin zabe da kuma kara bayar da muhimmanci wajen kula wa da sana’o’i da zaman lafiya a duk inda suka samu kansu

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.