Home / Labarai / Mun Gudanar Da  Ayyukan Raya kasa A 2022 – 2023 Masu Tarin Yawa

Mun Gudanar Da  Ayyukan Raya kasa A 2022 – 2023 Masu Tarin Yawa

…A karamar Hukumar Nangere.. Salisu Yerima

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Shugaban riko na karamar hukumar Nangere Honarabul Salisu Yerima ya bayyana cewar, sun gudanar da ayyukan raya kasa masu tarin yawa a karamar hukumar su daga shekarar 2022-2023.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin da Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Yobe ta fara ziyarar duba  ayyukan kananan hukumomin da aka aiwatar na 2022-2023 a kananan hukumomin Nangere, Fika da Potiskum a jihar.
Tawagar wacce shugaban kungiyar NUJ reshen jihar Yobe, Kwamared Rajab Mohammed Ismail ya jagoranta, na daga cikin kokarin ‘yan jaridu ke yi a jihar na tabbatar da gaskiya da rikon amana a gwamnatin Gwamna Buni a jihar.
Da ya ke jawabi ga  tawagar’ yan jaridun a ofishin sa da ke sabon garin Nangere shugaban rikon karamar hukumar ta  Nangere, Honarabul  Salisu Yarima  ya ce su a matsayin su sun gudanar da ayyukan raya kasa masu tarin yawa iya daidai gwargwadon matsayin su da suka hada da gina  ajujuwa 2 Hade da ofishi a Makarantar Firamare da ke Jakade tare da kammala gyaran gidan saukar baki na karamar hukumar da ke Sabon garin Nangere tare da sayen  janareta mai nauyin  30KVA, aka sa a wannan masaukin baki (LG Lodge) da sauran Kayayyakin alatu.
A cewar shugaban sauran ayyukan da majalisar ta aiwatar sun hada da gyaran bulo daya na ajujuwa 2 mai Hade da Ofis da ke kauyen Nzada, ginin makaranta mai azuzuwan 2 a garin Gabako sai gyaran gini mai azuzuwan biyu mai Hade da ofis a garin da kuma daya aikin kwaskware azuzuwan biyu a garin  Gwasko, da Garin Garin kolo duka a karamar hukumar ta Nangere.
Haka nan kan ruwan sha ma Majalisar dokokin a Nangere ta kuma yi aikin hakowa da sanya rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana” 6 da siyan janareta mai karfin 8HP ga Dorawa Katariya, Gyaran rijiyar burtsatse a sabon layi, Sayen kayan aiki, Siyan famfunan masu amfani da hasken rana masu nauyin 5Nos1.5HP da makamantan su.
Daga nan sai shugaban ya ce  dukanin ayyukan su sun kiyasta sun kashe zunzurutun kudi a shekarar 2022-2023 kusan kimanin Naira  N99,815, 000.00 kawo ya zuwa yanzu sun samu kashi 100 bisa 100 na kammaluwar ayyukan da suka sa gaba.
Ya kuma yabawa tawagar ‘yan jaridun karkashin shugaban kungiyar na Jiha Alhaji Rajab Muhammad dangane da wannan gagarumin aiki da suka dauka na jajircewa wajen duba ayyukan da kananan hukumomin jihar ke aiwatar wannan lamari tamfar tada musu tsimi ne don cigaba da gudanar da ayyukan raya kasa ga al’ a’ummomin su.
Tun farko da ya ke bayani dangane da makasudin wannan ziyara ta su, shugaban kungiyar ‘yan jaridun (NUJ) na kasa reshen Jihar Yobe Komred Rajab Muhammad ya ce sun shirya wannan ziyara ne don duba ayyukan da shugabannin kananan hukumomin ke aiwatar wa a matsayin su na wadanda suka fi kusa da al’umma wadda ya ce a shirye kungiyar ta ke don hada kai da shugabannin wajen gina jihar tare da tallata irin ayyukan da suke aiwatar wa ga al’ummomin su.
Ita ma a nata jawabin yayin da wannan tawaga ta ‘yan jaridu ta kai ziyarar duba ayyuka ga karamar hukumar ta shugaba riko ta majalisar karamar hukumar Fika kallabi tsakanin rauwuna  Hajiya Halima Kyari Joda ta godewa’ yan jaridun ne dangane da wannan ziyara da suka kawo don duba ayyukan su a karamar hukumar su ta Fika.
Daga nan sai shugabar ta dauki ‘yan jaridun ta zaga  da su don duba wasu daga cikin ayyukan da karamar hukumar su ta yi da suka hada da Ofishin ma’aikatar kula da aikin gona da suka kwaskware su da kuma duba wata katafila da ta fi shekaru 20 da lalacewa wadda majalisar karamar hukumar ta dukufa din gyara ta wadda shugabar ta ce ya zuwa yanzu sun kashe kimanin Naira Miliyan 3.1 don kokarin gyara wadda a yanzu sun cimma akalla kashi 30 cikin 100 da sauran ayyuka.
Hajiya Halima ta kuma tabbatarwa manema Labaran cewar ya zuwa yanzu karamar hukumar tunin ta kammala wasu ayyuka kamar;  magance zaizayar kasa a Balde, hana zaizayar kasa a kabano, gina sabuwar kasuwa  a Godowoli, gina wata cibiya kiwon lafiya  a Turmi, samar da kayayyakin koyo koyarwa da sayan hatsi, amfani da Peugeot 406 daidai da motar bas da dai sauransu.
Shugabar majalisar karamar hukumar Fika ta ce ya zuwa yanzu a shekarun 2022-2023 sun  kashe kimanin  kudi kusan naira miliyan 99,500, kuma sun kai kusan kashi 96 cikin dari wadda a ganin ta sun cimma gagarumar nasara.
Ta kuma nuna godiyar ta da kuma jin dadin bisa ga wannan ziyara da kungiyar ta NUJ ta shirya wadda hakan abin a Yaba ne.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.