Home / Labarai / MUN YI HANNUN RIGA DA GWAMNAN BANKIN NAJERIYA – GANDUJE

MUN YI HANNUN RIGA DA GWAMNAN BANKIN NAJERIYA – GANDUJE

Daga Imrana Abdullahi

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ko kadan su taron Gwamnoni da suka yi da shugaban kasa sun bayyana matsayarsu ta rashin amincewa da matakin da Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya dauka a game da batun canjin takardun kudin da aka sabunta.

Kamar yadda Abdullahi Umar Ganduje ya shaidawa manema labarai jim kadan bayan kammala taron Gwamnonin da shugaban kasa, sun ce za su koma jihohinsu su ci gaba da fadakar da jama’a cewa su ba su tare da tsarin Gwamnan Bankin Najeriya da wasu da suke zagaye da shi a kan batun canza takardun kudin da aka sabunta”.

Ya ce wannan ba tsarin jam’iyyar APC ba ne game da batun sake Fasalin takardun kudi da kuma mika kudin ga jama’a sam ba hannun APC a ciki kuma za mu ci gaba da fadakar da jama’ar mu domin kowa ya fahimta”.

Ya shaidawa manema labarai cewa ” kamar yadda kowa ya Sani shi ne Gwamnan Bankin Najeriya ya nemi takarar shugaban kasa amma bai samu hakan ba to, mai yuwuwa shi yasa hakan ke faruwa, don haka ba tsarin APC Bane”.

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I cewa ya yi a taron da suka yi da shugaban kasa an shaida masu cewa tsofaffin kudin da Bankuna suka karba a hannun jama’a sun fi yawan sababbin takardun kudin da babban Banki da kuma ma’aikatar da ke buga sababbin takardun kudi suka samar domin amfanin jama’ar kasa, wanda hakan ba abin da ya dace ba ne ayi”.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.