Home / Uncategorized / MUN YI NASARA A YAƘAR ’YAN BINDIGA, GWAMNA LAWAL YA SHAIDA WA BANKIN DUNIYA

MUN YI NASARA A YAƘAR ’YAN BINDIGA, GWAMNA LAWAL YA SHAIDA WA BANKIN DUNIYA

 

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya shaida wa Bankin Duniya cewa sannu a hankali, gwamnatin sa na samun nasara a kan ta’addanci a duk faɗin jihar.

A Juma’ar da ta gabata ne gwamnan ya kai wata ziyara ofishin Bankin na Duniya

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa tattaunawar da ta gudana tsakanin gwamnan da jami’an Bankin Duniyar, ta mayar da hankali ne wajen ci gaban fannonin ilimi, lafiya, noma da ɗumamar yanayi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa wannan ziyara ta gwamnan, za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Bankin na Duniya.

Cikin jawabin sa a wurin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ƙarfafa dangantakar ta Bankin Duniyar.

“Ina so in fara da nuna godiya ta ga Bankin Duniya game da tallafin da ya ke bayarwa a jihar mu. Mun jingina da manufofin Bankin Duniya wajen inganta rayuwar al’ummar mu kawar da talauci da ci gaban ayyukan inganta rayuwa.

“Muna sane da ƙalubalen da muka fuskanta, wanda ya shafi gudanar da ayyukan ci gaba a jihar Zamfara, musamman waɗanda suka samu matsala wajen aiwatarwa, sakamakon yanayin da aka shiga. Amma, lallai babu shakka muna samun ci gaba wajen magance matsalolin, lamurra na komawa daidai.

“Mun ɗauki ƙwararan matakai wajen magance matsalolin tsaron ta hanyar ƙara yawan ’yan sintiri da tsare-tsare don daƙile barazanar.

“Gwamnatinmu ta duƙufa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta hanyar samar da isassun kayan aiki da tallafi ga jami’an tsaro domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

Gwamna Lawal ya bai wa ma’aikatan Bankin Duniya tabbacin kare lafiyarsu a yayin ziyarar su, da suka haɗa da amintattun masauki, sufuri, da hanyoyin sadarwa mai kyau.

Gwamna Lawal ya bai wa ma’aikatan Bankin Duniya tabbacin kare lafiyarsu a yayin ziyarar su ta tallafi da sa ido a jihar Zamfara.

“Ina tabbatar wa Bankin Duniya cewa mun samar da hanyoyin da za a ci gaba da samar da tsaro don magance duk wata barazana da ta kunno kai da kuma tabbatar da kyakkyawan yanayi ga dukkan abokan hulɗar ci gaba.

“Mun daƙile hare-haren ‘yan bindiga a manyan titunanmu, ƙauyuka da garuruwanmu. A hankali muna samun nasara a yaƙin da muke yi da masu laifi, kuma rayuwa tana komawa daidai ga al’ummominmu. Wannan ya bayyana a cikin adadin al’amuran da ke faruwa a kullum da kuma yadda ake ƙara aiwatar da ayyuka cikin kwaciyar hankali a faɗin jihar Zamfara.

“Zan ƙarƙare da miƙa goron gayyatarmu ga Daraktan Ƙasa da ya ziyarci jihar Zamfara nan ba da daɗewa ba domin ganin an aiwatar da dukkan shirye-shiryen da Bankin Duniya ke tallafawa da kuma ƙoƙarin da muke yi na sauya yanayin jiharmu.”

Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Dr. Ndiame Diop, ya yaba wa Gwamna Lawal bisa yadda ya kyautata yanayin jihar Zamfara.

“Na gamsu da tsarin da ka sanya. Ina taya ka murnar samun irin waɗannan nasarori a cikin ƙanƙanin lokaci.”

A yayin taron, Jagoran NG-CARES ya bayyana irin nasarorin da aka samu a cikin tsarin aiwatarwa a Zamfara. “Ba wai a sauran jihohin Nijeriya muke ɗaukar irin wannan tsari na Zamfara ba, har ma muna miƙa shi ga wasu ƙasashe domin aiwatarwa, dole ne in yaba wa gwamna da gwamnatin jihar kan ƙoƙarin da suke yi,” inji ta.

About andiya

Check Also

Call Your Wife To Order, Niger Delta Groups Warn Uduaghan, Husband Of Senator Natasha

    ..Say outburst against Senate President Akpabio, shameful, unwomanly A coalition of groups from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.