Bashir Bello majalisar Abuja
Honarabul Bello Hassan Shinkafi dan majalisar wakilai ne ta tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi a majalisar wakilai ya bayyana irin abin da ya faru a garin Magarya da cewa abin takaici ne da aka kashe yan Sandan Najeriya har guda Bakwai.
Bello Hassan ya ce wadannan mutane yan Ta’adda sun yi angaya bisa Babura da yawan gaske suka kashe yan sanda guda Bakwai tare da Kone makarantar sun kuma shiga cikin gari sun harbi mutane uku sun kuma kwashe dimbin Dukiya mai yawan gaske.
” A wannan gari na Magarya saboda Yan Sandan da aka kai a kullum zaka ga kauyuka wajen Hamsin da ke zagaye da Magarya suna zuwa gudun hijira a wannan kauye domin tsira da rayukansu kuma a wannan garin Shanunsu da duk Dabbobinsu duk a wurin suke ajiye su baki daya, amma wadannan barayin sun ta fi da Dabbobi ba iyaka kuma sun ta fi da wadansu mutane daga garin”.
Honarabul Bello Hassan ya ci gaba da cewa babban dalilin da yasa ya kira taron manema labarai a Abuja shi ne ya na ganin laifin yan jarida domin ni ba zan iya ganewa ba ana kin yayata abubuwan Jihar Zamfara a game da irin wadannan abubuwan da ke faruwa suk da cewa Gwamnan Jihar Zamfara na yin iyakar kokarinsa kuma duk abin da zai kawo zaman lafiya a Jihar ya na yin sa koda kuwa kasafin kudin Jihar zai kare ne ya na yin sa a koda yaushe a koda yaushe a shirye yake ya yi shi kuma ya na cikin yin sa”.
” Amma laifin da muke gani na yan jarida a nan shi ne baku yin kokarin kawo rahoton da yakamata a sanar da duniya domin kowa ya Sani a kawo dauki a wannan Jihar ta Zamfara, abin da nake gaya maku a halin yanzu a mazaba ta karamar hukumar Zurmi ta fi komai shiga cikin tashin hankali domin zaka iske kauyuka a yanzu haka ba za su iya tafiya Noma sai sun fanshi kansu kauyen da ake cewa sai ya biya miliyan Takwas, miliyan Goma, miliyan Talatin kai har Arba’in ana Dorawa mutane. Kuma ni kaina a satin da ya gabata na je irin kauyen kaiwa lamba da naje ta’aziyya inda suka shiga suka koma motocin garin suka Kona abincin garin kuma suka ta fi da mutum dari da uku (103) kuma mutum Tamanin da uku cikinsu duk mata ne har yau mutanen nan suna can a wurinsu ana jiran ma su yi magana su fadi abin da suke so, a garin ja Banda da shima naje tsakanin Jabanda da Kwabre nan ma an dauke mutum sha biyar a cikin mutanen nan akwai mata da kananan yara to, wannan wane irin abu ne don haka muna yin kira ga jami’an tsaro na Najeriya da du ji tsoron Allah su san abin da yakamata a kan kananan hukumomin Zurmi da Shinkafi da kuma Jihar Zamfara baki daya lallai su taimaka.
Bello Hassan ya ci gaba da yin kira ga shugaban rundunar Sojan Najeriya da duk abin da za a yi a taimaki jami’an tsaron nan da kayan aiki to lallai ayi kuma wadanda aka kai muna godiya kwarai amma muna neman karin jami’an tsaro.
” A yau Jihar Zamfara ga Soja ga yan Sanda amma mutanen nan suna ta yawo a duk inda suka ga dama a inda suke so a koda yaushe, ga rahoto ya kawo ga labari ana ji amma zaka ga kowannensu na jiran a ba shi izini domin ya yi aikin sa na tabbatar da tsaro don haka ne muke yin kira lallai maganar nan ta sai an bayar da izini ya dace a kara duba ta sosai me yakamata ayi. Na san dukkan sojojin da muke da su kowanne na da iyakar yankin da aka tura shi ya yi aikinsa to, wannan lamarin aba kowane damar yin aiki duk abin da ya faru sojan da ke wurin me ya faru a wurinka amma duk wannan dole ne sai an ba su jami’an tsaron isassun kayan aiki da isasshen Albashi da kuma alawus – alawus na san ana ba su Albashi da alawus amma a tabbatar ya na zuwa wurinsu hakan ne za a yi a ciyo kan wannan lamarin domin ni da na tashi a yau hankalina ya tashi saboda haka ne tun da safe na taso na samu shugaban majalisa domin in gabatar da kudirin hakan a majalisa amma lamarin bai yi ba don akwai wata ka’idar da ya dace abi kuma na amince da shi ya kuma ba ni hakuri wanda idan Allah ya kaimu sai mutum ya gabatar. Sakamakon hakan ne na ga dacewar mu hadu da ku a wajen taimaka mana da Jihar Zamfara .
Kuma ina son tabbatar wa duniya cewa a halin yanzu an dauko hanyar kawo karshen wannan matsalar a Jihar amma lamarin na bukatar a kara taimakawa.
Ina yin kira ga daukacin jama’ar da wannan lamarin ya faru a kan su da su ci gaba da yin hakuri domin ina tabbatar masu cewa yadda suke jin wannan abu a cikin zuciyarsu ni ma haka nake ji kwarai tun jiya da Dare da aka gaya Mani cewa ga su nan zuwa ban runtsa ba ina ta tunanin al’ummar da suka zabe mu amma ina kara yin kira ga sauran jama’a da su ji tsoron Allah domin a cikinsu akwai wadanda suke taimakawa wadannan mutane domin an kama daya an kama biyu an kama uku kuma su rika yin kokarin taimakawa jami’an tsaro da bayanai hakan zai iya taimakawa a samu zaman lafiya sannan a ci gaba da dagewa da addu’a cewa wadannan mutanen da aka Sani da wadanda ba a Sani ba muna rokon Allah ya Tina masu asiri Allah ya kawo karshen abin kuma duk wanda ke yinsa Allah ya mayar da abin a cikin gidansa da karan kansa