Home / Big News / MUNA DA KYAKKYAWAR DANGANTAKA TSAKANIN MU DA GWAMNATIN JIHAR BAICHI – ABDULLAHI HASSAN

MUNA DA KYAKKYAWAR DANGANTAKA TSAKANIN MU DA GWAMNATIN JIHAR BAICHI – ABDULLAHI HASSAN

 Abdulllahi Hassan shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikata na Jihar Bauchi, a tattaunawar da ya yi da wakilin mu ya bayyana wa duniya irin yadda Dangantaka, batun Albashi da kuma batun mafi karancin Albashi sauran al’amuran da suka shafi ma’aikata musamman wadanda yake yi wa jagoranci, ayi karatu lafiya.
A MATSAYINKA NA SHUGABA NA MANYAN MA’AIKATA A JIHAR BAUCHI ME ZA KA IYA YIN BAYANI DANGANE DA BIYAN ALBASHI A JIHAN ?
Azahirin gaskiya dangane da maganan albashi a jihar   Bauchi sai dai muce Alhamdulillahi, saboda gwamnatin jihar a gaskiya tana kokarin biyan albashi akan lokaci, domin kuwa babu watan da muke bin gwamnatin jihar Bauchi albashi, domin kuwa ko wane wata gwamnatin jihar Bauchi tana biyan mu albashi a kan lokaci. Sai dai abubuwan da ba’a rasa ba game da masu korafi da dan damuwa nan da can, masu matsalar PSN lamba, ko na lambar asusun banki, ko an mutu, ko na wani, wanda dai ko wane wata akan samu haka, wannan kuma shine dalilin da ya sa akace ko wane  wata a dinga kawo sakamakon irin wadannan matsalolin domin gaggauta magance su, sai an samu an gyra kafin a biyasu.
TO SU WANE NE YA KAMATA SU DINGA KORAFI A KAN BIYAN ALBASHI?
Alalhakika mu ne dama yan kungiyoyi ya kamata mu dinga korafi idan gwamnatin ta gaza wurin biyan albashin. Mu kuma mun san da cewa gwamnatin jihar Bauchi tana iya bakin kokarin ta domin taga ta biya daukacin ma’aikatanta albashin su akan lokaci, don bamu da wani korafi akan maganan rashin biyan albashi, gwamnatin jihar Bauchi tana biyan albashi ba tare da wani jinkiri ba.
KO WANE BAYANI ZA KA YI A KAN WASU JIHOHI TAWAJEN KYAUTATAWA BIYAN ALBASHI MUSAMMAN KAMAN ABIN DA YA SHAFI ALBASHI MAFI KARANCI NA NAIRA DUBU TALATIN DA KUMA SHAWO KAN MATSALOLIN?
Anan dai babu abinda zan ce a gaskiya sai Alhamdulillahi domin kuwa gwamnatin jihar Bauchi tayi rawan gani wanda bamu san me zamuce mata ba sai dai fatan alkhairi. Allah Ya kara mata kwarin gwiwa a kan abinda take yi. Yanzu in ka fita jihohi da dama, wanda duk sukai karin wannan naira dubu talatin din na mafi karancin albashi duk sun janye sun koma yanda ake yi da, wasu kara ragewa sukayi a kan yanda ake biya tun farko, a sakamakon ballewar  annobar cutar sarkewar numfashi wato (Corona) an sami matsala na tabarbarewan tattalin arziki, hakan ya yi nasaba wajen janye wannan mafi karancin albashi. Amma duk da hakan mu a jihar Bauchi Allah Ya taimake mu domin kuwa har yanzu mai girma gwamnan jihar Bauchi bai girgiza ba yana kan kudurinsa na cigaba da biyan wannan mafi karancin albashi wato naira dubu talatin, bugu da kari shima hidimar warware matsalolin biyan albashin a yanzu haka maganan da nake maka anyi nisa da wannan maganan domin kuwa har anyi nasasar kaiwa shi mai girma gwamnan, ya yaba, sannan ya kara da cewa aci gaba da gyara abun yanda kowa zaiji dadi sannan al’ummar jihar su amfana da wannan tsarin.
WANI KARIN HASKE ZAKA YI A KAN KOKARIN DA GWAMNATI KEYI NA BIYAN ALBASHI DA ZARAN WATA YA KARE?
Ka san wani baisan ma ya akeyi gwamnati take samu ta biya albashi ba. Shi da zarar yaji ance wata ta kare ba zai yi la’akari da wai shinma ita gwamnatin ana bata kudin da za ta biya albashin kuwa, shi dai daga wata ta kare sai ya fara tada jijiyan wuya ya ce shi yana jiran albashi.  Toh akwai abinda ake kiranshi (FAC) in akaje akai (FAAC) dinnan kudin da suke zuwa su karbo a wajen gwamnatin tarayya dinnan ba fa rige-rige suke yi tsakanin kudin da kuma wanda yake wakilci wurin wannan taron ba, sai fa anzo an zauna an yi cike-cike da dai sauransu, hasali ma in da za’a biye wa tsarin FAAC din ne wallahi albashin na ko wane wata sai ya cimma wata watan kafin a iya samu a biya albashin, amma gwamnatin jihar Bauchi ta tsaya tsayin daka tana kare mana iya muradin mu tana kare mana hakkin mu na ma’aikata, tana kare mana muradin mu na kungiyar kwadago wato (NLC) hasali ma ta kan kira bankuna azo a zauna ayi yarjejeniya kafin kudin su sauka za ka ga har sun daidaita an fara biyan albashi, don haka gaskiya gwamnati tana bakin kokarinta akan wannan.
KO INA GASKIYAR  MAGANAN DA AKE CEWA KO WACE MA’AIKATA ITA KE BIYAN ALBASHIN MA’AIKATAN TA?
Toh ai ranan wanka ba’a boyon cibi, abunda nake son fada maka a matsayinka kai ma na dan jarida don ka kara samun karfin gwiwa, ka tashi ka je ofishin shugaban ma’aikata, akwai wani daki da ake kira (Situation Room) ka je wajen idan wata ya kare kazauna a wajen, ni Wallahi na baka wannan daman, za kaga ko wane ma’aikata suna zuwa suna biyan albashinsu, ko wace ma’aikata albashin ta ya koma hannun ta, in ta ga dama ta zo ta biya da wuri, in ta ga dama kar ta zo ta biya da wuri, haka zalika an cire manyan ma’ikata guda hudu a ko wace ma’aikata wanda su za suzo, akwai mai binciken bayanai, da mai daura bayanai wato (uploading) da mai dubawa da kuma mai yarda a biya. A kowane ma’aikata an fidda wadannan mutum hudun, saboda duk wani abu ya koma hannun ma’aikata, in kaga ma’aikaci bai samu albashi ba toh laifin ma’aikatan sa ne, in kaga ma’aikaci an ce wai ba a sa masa kudin wani abuba laifin daga ma’aikatan sa ne, ko an yi albashi bai samu ba nauyin na wuyan ma’aikata ne tsakaninta da ma’aikatanta. Don haka a gaskiya na ji dadin wannan tambayan naka don Wallahi yanzu Jihar Bauchi ta zamo tauraruwa wajen tsare mutuncin ma’aikatan ta da albashin su, in kuma kaga an samu matsala toh daga ma’aikata ne ita gwamnatin tayi iya bakin kokarin ta, kuma ta dauki yarda ta mika wa ma’aikata, in kaga dama ka gyara in kaga dama kar ka gyara, ta dauki amana ta ba ka in ka ga dama kaci in kaga dama ka gyara.
AKWAI WASU DAGA CIKIN YAN JIHAR BAUCHI ZAKA GA SUNA HAWA KAFAFEN SADA ZUMUNTA SUNA RUBUCE-RUBUCE A KAN ALBASHI, KO ME ZAKAI KARIN HASKE A KAN WANAN BATUTUWAN?
 Toh Alhamdulillahi naji dadi dakamun wannan tambayan, kafafen sada zumunta yanzu yazamo wani fage ne wanda zance wato fadi sonka, saboda kwanannan ma muka gani a kafafen sada zumunta wai mu yan kungiyar kwadago wato (NLC) wanda bamusanda wannan kungiyarba kuma bamusan wannan mutumin ba, munga wani wai “BalanGoggo62” shine yake cewa wai “gwamnatin jihar Bauchi takai wata takwas bata biyan albashi”, toh abin yabamu mamaki matuka, ta inda yasamo wannan labari, yakamata idan zaka fadi abu karinka bincike kasan mene ne gaskiyan al’amari kafin ka fadeshi, azahirin gaskiya gwamnatin jihar Bauchi ba’abinta albashi na wata ko daya, domin kuwa tana biyan albashinta akai-akai.
Kuma kasan mu wani lokaci kaman Dansanda(police)ne zakaji yace ina aiwatarda aiki na amma ba wanda ya aminta dani, mu yan kungiyar kwadago (NLC) anaganin kaman kawai muna zaune kawai bawani aikinda mukeyi, bamu tuhumar gwamnati, bamu tashin hankali da gwamnati, bamucewa atafi yajin aiki, toh alalhakika mutane basu gane cewa ko yakine akeyi, azo azauna a teburin shawarwari shine ake samun mafita, haka zalika ko mene yataso inba kazauna a teburin shawarwariba bazaka taba samun mafitaba, kazo kaita fadan maganganu kala kala a kafafen sada zumunta ko a gidan radiyo kana sukar gwamnati wannan bayida wani amfani kuma bazai samarda cigaba ba, mu yan kungiyar kwadago wato (NLC) muna yawo jaha jaha munkuma San abunda jahohi da dama suke ciki, wallahi bazan fadi sunan jahar bane, amma haryanzu akwai masu daukan albashin naira dubu takwas ajihar,  zakaji ana kwarzanta jihar amma  akwai masu karban albashin naira dubu takwas.
Amma mu gwamnatin jihar Bauchi  bakaman kananan ma’aikata idai bazasu zauna suyi Alwalla suyi sallah su godewa Allah ba, toh saidai ace kawai suna korafin son ransu ne, saboda yanzu kaga da matakin aiki na daya zuwa na shida sune suke morewa wannan mafi karancin albashi na naira dubu talatin din, daga mataki na bakwai zuwa sama kuma sune aketa kokarin ganin sunhau wannan tsarin suma.
Amma saikaga wani yazo ya fake yana fadin son zuciyarsa. Bari inbaka labari akwai randa naje gona na iske mai gonan suna rikici da wanda yai masa aiki, saiyace wai wallahi gwamnatin jihar Bauchi ne bata biyashi albashin shi ba, danaje nace to ni dan kungiyan kwadago ne (NLC) ka kawomun sunanka da bayananka zansa ataimaka abiyaka albashi, wallahi dana kureshi saiyace shifa gaskiya ba ma’aikaci bane yagane kawai kowa dawanman yake kare kansa yace ai gwamnati ne bata biya albashi ba. Kaga duk irin wannan bayida amfani, kadunga tsayawa kana fadin gaskiya dangane da abunda yashafi gwamnati. Akwai wanda zakaga  sun kafa kungiya suna zuwa zauren mutane suna cewa anrike albashi,  gwamnatin jihar Bauchi bata biyan fansho kaza-kaza… wannan fadi sonka kawai sukeyi, inason infada maka wallahi ni tsohon ma’aikaci ne, akwai gwamnatin da sojoji ne da bulala ahannunsu suke samu a alayi ana tantancemu, babu gwamnatin da intazo bata wannan tantancewar amma kawai sai mutum yazo yamaida wani abu sabo kaman wanda ba’atabayin irin wannan abunba. Bawai za’ace ita gwamnatin abunda takeyi dari bisa dari dai-dai bane, ba haka bane, kuma daman inkazo magana gyara dama gyara haka ne, duk lokacinda akace anzo gyara akan wani abu toh wallahi tallahi dole asamu antaba mai kyau da mare kyau, amma mu abinciken mu da dama damukayi acikin kashi dari na masu korafinnan duk wanda kaji antaba masa albashi, inka binkici abun saika samu lallai shima yanada matsalarsa wanda yasani saiya fake sai abin ta fito yafara maka kame kame, don haka mu yan kungiyar kwadago (NLC) koma waye yafadi abunda ke ransa amma dai mu mun san da zaran aka ce maka kungiyar kwadago bata tasiri ko da na awa daya ne a cikin jihar Bauchi Wallahi kowane ma’aikaci sai ya gane kuskuransa, suna ganin kaman mu ba mu aiwatar da komai ne, kowa muna da labarin sa dai dai gwargwado, za ka zo ka gama maganan ka ka gama meye-meye din ka sai dai muji ka kawai mu yi shuru, dan kungiyar kwadago (NLC) ba mahaukaci ba ne, ba anyi shi kullun ya zo ya zauna yaita surutu a radiyo yana cewa kaza-kaza ba ne, a a, dan union yana amfani da gundarin gaskiyar sa ne. Ka tabbatar da gaskiyan ka kafin ka yi magana.
Yanzu kwanan nan ma wani ya ke cewa wai zuwan Atiku Abubakar jihar Bauchi, gwamnatin jihar Bauchi ta kasa biyan albashi, wa ya fada maka, an yi (PAC) ma tun kafin Atiku ya zo, zuwan Atiku shi ne zai sa a kasa biyan albashi, in banda mutane, yanzu sai ace mutum za ka yi bako a gidanka ko a wani abun naka sai kace wai don zuwan bako ne ba za aci tuwo a gidanka ba ko dan kacyi bako an kasa cin tuwo a gidnaka kenan, saboda haka mutane su dinga magana wanda ya dace wanda hankali zai dauka, ba wai kawai mutum ka fito kaita magana sararara ba, ba tare da hujja ba.
Duk wani mai kishin jihar Bauchi, kowa ya shigo jihar Bauchi ya san Bauchi ta canza, ansamu canji a jihar Bauchi, kuma babu abinda zamuce sai dai muce gwamnatin jihar Bauchi Allah Ya kara mata karfin gwiwa taci gaba da wannan abun, ba kuma na zo gidan radiyo inyita koda gwamnati ba ne, face na zo ne in fada gaskiyan abinda ya ke faruwa, ni dan kungiyar kwadago ne wato (NLC) ba na zo in yi kamfe wa gwamnati ba ne amma dai ni ina fadan gaskiyan abunda yake faruwa ne.
Gwamnatin jihar Bauchi ta na mana iya kokari, Ubangiji Allah Ya sa mudace, Gwamna kuma ba shi kadai yake wannan abun ba face da hadin gwiwa da kuma jajircewar mukarraban sa da suke kokarin a ko da yaushe su ga sun sa shi a hanyar dai-dai, Ubangiji Allah Ya taimakesu, Allah Ya sa a dace. Kuma ina kara jawo hankalin mutane kafin ka fito kai magana dangane da maganan ka kushe gwamnati ka je ka yi bincike ka samu gaskiyan al’amari sannan ka zo ka yi magana.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.