Home / News / Muna Goyon Bayan Matakin Da Dallatu Muktar Ramalan Yero Ya Dauka Na Komawa APC – Jagororin Tafiyarsa

Muna Goyon Bayan Matakin Da Dallatu Muktar Ramalan Yero Ya Dauka Na Komawa APC – Jagororin Tafiyarsa

Daga Imrana Abdullahi
Honarabul Nasiru Dogara daga karamar hukumar Zariya ya bayyana cewa sun fice daga jam’iyyar PDP ne domin jaddada cikakken goyon baya da hadin kai tare da nuna ana tare da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Dokta Muktar Ramadan Yero, domin ba yadda Daki zai tashi ragaya ta zauna.
Nasiru Dogara ya shaidawa manema labarai jim kadan bayan da suka kammala taron tattaunawa da tsohon Gwamna Muktar Ramalan Yero, a gidansa inda suka amince da shawarar ficewa daga PDP kasancewa kamar yadda Dogara ya ce   ba yadda Daki zai tashi ragaya ta zauna.
“Kowa ya Sani a jam’iyyar PDP Mai girma Dallatun Zazzau Alhaji Muktar Ramalan Yero ginshiki ne kuma jagora ne kuma kamar irin mu da muka dade a cikin hidimar sai mu zauna hakika ba mu yi wa kanmu adalci ba kuma ba mu yi wa mabiyan mu adalci ba, wannan na daya daga cikin dalilan da suka Sanya muka yanke hukuncin barin jam’iyyar PDP domin mu shi.
Shima a nasa jawabin Hassan na kungiyar Yero Contact, cewa ya yi sun kafa ainihin kungiyar Dallatu Forum ne domin tallar manufofi na Dallatu tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, tun a shekarar 2015 suke hidimar Dallatu zalla har zuwa yau 2023.
Hassan ya ci gaba da cewa tin da dai ya bar jam’iyyar PDP sai suma suka ajiye tafiyar domin ya koma APC lallai duk mambobin Yero contact duk a inda suke mun yanke shawarar komawa APC somin mu bi shi.
Daga yau duk mai son jin ina Dallatu ya sa gaba ya koma APC tare da mu duk yan Yero Contact a duk fadin Jihar Kaduna baki daya.
Sai ya yi kira ga daukacin yayan kungiyar da su ninka irin gudunmawar da suka yi wa Dallatu a can baya lokacin suna PDP, a yanzu a ninka gudunmawar a APC domin a samu nasara, siyasa ake yi shima tare da mu baki daya siyasar zamu yi, muna yi mashi fatan alkairi kuma muna yi masa fatan alkairi a koda yaushe.
“A kungiyar Yero Contact muna da wakilci tun daga Akwatunan Zabe, Gunduma zuwa matakin kowace karamar hukuma, akwai kuma kwamitoci Goma sha tara a cikin wannan kungiyar, muna jaddadawa jam’iyyar APC cewa za a ga aikin mu a ko’ina
Malam Balarabe Jaji, wani tsohon dan Gwagwarmayar siyasa ne da ya bayyana wa manema labarai cewa sun yi siyasa tun zamanin marigayi Dabo Muhammad Lere a matsayin jagora daga nan sai ya hannatashi zuwa marigayi Sanata Muktar Ahmad Aruwa, daga nan shima marigayi Aruwa ya hada ni da Muktar Ramalan Yero saboda haka dukkan abin da zaka yi a rayuwa kana neman mutunci to, muktar Ramalan Yero mutum ne wanda ya san mutuncin jama’a ya san mutuncin dan Adam kuma ya na da kishin jama’ar shi da al’umma da kasa baki daya don haka duk mutumin da ya hada wannan dole ne ka rike shi ya zamar maka jagora saboda hakan ne muke tare da Dallatu tun shekarar 2015 yana a kan kujerar Gwamna muka nema Allah bai bashi ba kuma muna tare da shi 2019 ma muna tare da shi 2023 muna tare kuma a yanzu ma muna tare da shi sai yanayi ya bayar cewa ya ga ya dace ya bar jam’iyya PDP tun da ya ce ya bari muka ce mun bari muna jiran lokacin da zai yanke shawarar inda zai ta fi, yau kuwa ya kira mu ya ce ya yanke shawarar zai shiga jam’iyyar APC kuma dukkannin mu Jagororin tafiyarsa lokacin siyasa muka daga yankuna Uku na Jihar Kaduna da suka hada da shiyya ta Kudu, Arewa da Tsakiya duk muna tare kuma min yanke shawara mun shiga jam’iyyar APC.
“Kuma mun je mun hadu da mai girma Gwamna kuma yadda Gwamna ya Karrama mu ya fadi wadansu halaye da mai gidan mu da kuma abin da suka hango lokacin mai gidan mu ya tsaya takarar Gwamna suna ganin idan da shi ne Allah ya bashi takarar nan da sai an sha bayar wahala koda APC za ta samu nasara amma da Allah yasa ba shi ne dan takara ba sai suka zauna kawai hankalinsu a kwance wannan ita ce kalmar da Gwamna ya fadi, ga shi yanzu ya dawo da jama’ar da Allah ya bashi Malamai da sauran al’umma za mu taru mu ci gaba da yi wa APC hidima ta kara kafa Gwannati a Jihar Kaduna da tarayyar Najeriya baki daya da izinin Allah

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.