Home / KUNGIYOYI / Muna Kira Ga Gwamnati Ta Nemawa Sa’adiyya Idris Hakkinta

Muna Kira Ga Gwamnati Ta Nemawa Sa’adiyya Idris Hakkinta

An Yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I da ta tabbatar da an hukunta wani Malamin addinin Kirista da ya dauki wata yarinya mai suna Sa’adiyya Idris, ya mayar da ita yarsa da kuma canza mata addini daga matsayinta na musulma zuwa Kirista.

Wannan kiran ya fito ne daga bakin Malamin addinin musulunci Shaikh Yusuf Musa Asadussuna, lokacin da yake ganawa da manema labarai a cibiyarsu da ke Kaduna.

Shaikh Yusuf Musa Assadussuna, ya fadakar da Gwamnati ta hanyar tuna wa jama’a irin yarjejeniyar da aka yi a can baya cewa duk wanda aka samu da aikata laifi irin wannan ko daga wane bangare yake lallai Musulmi su yi hakuri a hukunta shi domin abin ya zama darasi ga na baya.

Ya ce haka lamarin yake lokacin da aka cimma matsayar cewa idan an samu wani ya aikata irin wannan laifi ta hanyar da bata dace ba ya mayar da wani cikin addinin Kirista to a hukunta shi domin ya zama darasi ga saura.

“Na san an yi ta kokarin a cimma sulhu a samu matsaya tsakanin bangarorin biyu na ita yarinyar da kuma dayan bangaren a gaskiyar magana ba a samu cimma matsaya bane, da kuma yarjejeniyar da yakamata, saboda haka muna ganin yarinyar nan marainiya ce sai mu yan uwanta ne musulmi domin mahaifinta ya rasu to hakki ne a gare mu mu tabbatar mun karbo mata yancinta.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin tarayyar Nijeriya baki daya da cewa a daina yin sakaci idan irin wannan abu ya faru ga wadansu a kasa a hukunta su, misali da cewa akwai Malam Abdullahi da ya musulunta wanda asalinsa shi ba musulmi bane musulunta ya yi amma akwai yarsa da suka Haifa tare da matarsa kafin ya musulunta, ita kuma bata shiga musulunci ba amma har yanzu sun ki amincewa yasa yarsa da ya haifa da cikinsa yasa ta a idanunsa. Ai akwai alaka ta haihuwa ko an raba addini wanda a yanzu sai dai alaka ta waya kawai babu damar ya ga yar da ya haifa da cikinsa saboda sun raba addini. Irin wannan matsalar kuma ta faru da Yunusa Yellow, yarinya ce ta musulunta aka daura aure a tsakaninsu amma daga baya sai ga wasu sun tayar da rigima cewa wai ya kwace yarinyar ne ya canza mata addini shekarunta bai kai ba kowa na ganin yadda aka dauke shi aka kai Kotu aka daure shi a gidan Yari.

Shi yasa muke kira ga Gwamnati da ta daina bari daidaikun mutane na daukar doka a hannunsu, yin hukuncin da ya dace shi ne mafita, amma idan Gwamnati bata daukar mataki idan abu ya faru to su kuma mutane za su yi abin da bai kamata ba mu kuma shi ne abin da bama so Allah yasa mu dace.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.