…Alhaji Hassan Ya Dauki Nauyin Marayu 10 su haddace Kur’ani
Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Hassan Abubakar ya jawo hankalin iyayen yara masu yin halin ko’ in kula game da tarbiyyar yaya da su Sani cewa ba wanda fa zai iya daukar nauyin yayan wani ko wasu haka kawai don haka yin watsi da yaya ba tsarin musulunci ba ne.
“Kamar yadda kowa ya gani a halin yanzu an ga irin yadda yara ke yin karatun Alkur’ani yaran nan suna zaune a gida har sun yi saukar yin hadda kuma suna da ilimin zamani na jami’a ma duk baki daya.
“Saboda haka babu wata hujja da wani zai yi amfani da ita ya dauki yaronsa haka kawai ya kai shi almajiranci ya je ya nemi ilimi hakika wannan ba gaskiya ba ne. Kawai ana fakewa ne da Guzuma a harbi Karsana kawai, wanda kuma su ne musabbabin abin da ya Jefa arewacin Najeriya cikin fitinar da ake ciki a yanzu.
Don haka ayi kokarin yin maganin wannan matsalar da nufin kawo karshen ta baki daya, Malamai su ji tsoron Allah su daina cewa idan an ce a daina almajiranci ana yaki ne da karatun Kur’ani ba. Duk Malamin da aka kaiwa yara domin su yi karatu ya dace a Sani cewa shima fa Malamin na da nasa larurorin amma ba a bashi kudin abinci ba duk da cewa idan mun kai yayan mu makarantun kwana na Boko muna biyan kudi kamar yadda aka Dora ma iyayen su biya, saboda haka me yasa ba za a yi wa karatun Kur’ani ba? duk da cewa shi ne babban jigo kuma mafita duniya da lahira , iyaye su rike karatun yayansu, domin shi ne mafita duniya da lahira.
Muna kuma yin kira ga iyayen yara da a Sani cewa idan sun haddace Kur’ani ba wai ya zamo cewa hafizai ko alarammomi ba su Sani cewa fa yanzu za su fara, sannan kuma su cire girman kai su kuma ji tsoron Allah su san cewa sun yi wannan ilimin ne ka tsoron Allah ba wai neman suna ba, ba kuma na zuwa masabaka ba su yi kokarin yin amfani da karatun wajen neman tsira duniya da lahira.
Alhaji Hassan, ya kuma yi kira ga iyaye da cewa su rika fahimtar cewa ba tarin kudi ko wata Dukiya ba ne abin yin la’akari a rayuwa ba, kawai jajircewa wajen ilmantar da yaya ne ta hanyar ba su ingantaccen ilimi wanda zai rike su duniya da lahira domin idan yara sun samu ilimi duk matsalar da ake fama da ita ta rayuwa ta fuskar kalubale musamman ta fuskar harkar satar jama’a ba za a samu hakan ba. Saboda haka idan iyaye sun sauke nauyin da Allah ya Dora masu hakika za a samu ingantacciyar nasara, muna kyautata zaton cewa za a samu saukin wannan al’amari kuma musan cewa hakki ne a kan mu kamar yadda malamai ke fadi cewa yayan mu abin kiwo ne a gare mu kuma Allah zai tambaye mu a kan abin kiwon mu”.
Daga cikin daliban da Alhaji Hassan Abubakar ya dauki nauyin karatunsu sun hada da Abubakar Isyaku dalibin da ya haddace Kur’anin dan shekaru 15 da ya yi shekaru hudu 4 yana yin hadda kuma Allah ya tabbatar da an yi nasara.
Sai kuma Asma’u Hassan Abubakar da ita ma ta yi shekaru hudu (4) ta na yin HADDAR Alkur’ani kuma ita ma ta samu nasarar da kowa ke bukata na haddace kur’anin cikin nasara.
A bayanan da suka gabata na tabbatar da cewa wannan bawan Allah Alhaji Hassan Abubakar ya dauki nauyin karatun marayu mutane 10, domin su haddace Kur’ani mai tsarki, abin da ya dace ayi ko yi da shi a cikin al’umma.