Home / Labarai / Muna Kira Ga Malamai Da Su Yi Wa’azi Ba Tare Da Tashin Hankali Ba – Yusuf Ibrahim Zailani

Muna Kira Ga Malamai Da Su Yi Wa’azi Ba Tare Da Tashin Hankali Ba – Yusuf Ibrahim Zailani

….Da fatan Za’a yi bukukuwan Sallah lafiya

Daga Bashir Bello Dollars

Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani Wakili ne daga karamar hukumar Igabi a majalisar dokokin Jihar Kaduna ya yi kira ga daukacin Malamai da su rika yin wa’azin musulunci ba tare da tashin hankali ko tsangwama ba domin shi addinin musulunci Nasiha ne kuma Nasihar nan ita ake bukata a koda yaushe, Allah ya zauna da Najeriya lafiya da Jihar Kaduna lafiya kuma Allah ya ba shugaban kasa da mataimakinsa lafiya kuma ya ba su ikon tausayawa talakawan Najeriya a kuma yi ayyuka na alkairi da za a ce gara sa aka yi wannan Gwamnatin, Allah ka shige masu gaba ka iya masu kada ka barsu da iyawarsu ya kuma yaye mana musibun rashin tsaron da ke damun kasar nan Allah ka ba mu mafita ba domin mun isa kai ne Ahadussamadu huwarrahmanu

Zailani ya kuma yi karin bayani kamar haka, “Mun godewa Allah mai kowa mai komai da ya kawo mu wannan rana ta karamar Sallah kasancewar akwai wadansu mutane da a halin yanzu ba su samu damar ganin wannan rana ba, da muka gani a yau”.

“Ina kuma ta ya Musulmin duniya baki daya murna da Allah ya amince suka yi Sallar Idi a yau kasancewar wadansu da yawa sun ta fi lahira amma mu muna cikin yantattun bayinsa har ya bar mu aka yi Sallar Idi da mu don haka ne muke yin godiya da wannan ni’imar da ya yi mana. Ko wannan Azumin na kwanaki Talatin alfarma ce Allah ya yi mana”.

Honarabul Zailani ya kuma ce ya na yin kira ga mutanen mu da ayi shagalin bikin murnar Sallah lafiya ba tare da fitina ko wani al’amari daban ba ta yadda za a samu ci gaba a Jihar Kaduna da kasa baki daya.

About andiya

Check Also

AGILE project trains 2,400 on schools improvement plans in Sokoto 

By; S. Adamu, Sokoto A socio-education project driven organisation , the Adolescence Girls Initiative for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.