Home / Big News / Muna Rokon Gwamnati Ta Bamu Damar Yin Sallar Juma’a

Muna Rokon Gwamnati Ta Bamu Damar Yin Sallar Juma’a

Imrana Abdullahi
Sanannen Malamin addinin musulunci Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun, ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna a matsayinsa na shugaba kuma babban jami’in tsaro a Jihar da ya ba musulmi da Kiristoci a kalla Awoyi biyu zuwa uku ranar Juma’a da Lahadi domin su gudanar da Ibadarsu a wuraren da suka saba aiwatarwa.
Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a kaduna, inda ya ce hakika ya dace ayi la’akari da cewa ana yin mulkin Dimokuradiyya ne don haka jama’a na bukatar a ba su yancin yin Idarsu koda na yan Awoyi daga biyu zuwa uku ne.
“Mu yin Ibadar nan ya fi mana komai domin daman saboda Ibadar ne Allah Madaukakin Sarki ya halicci dan Adam, don haka muna kara yin kira hade da roko a bamu damar yin wannan Ibada”.
Sambo Rigachikun ya ci gaba da cewa duk in da aka ba musulmi awayi uku sun kammala Sallar Juma’ar da za su yi baki daya, haka suma yan uwa abokan zama Kiristoci a ba su irin wannan damar a ranar Lahadi su gudanar da tasu Ibadar.
“Malaman da suke gani bai dace a bude masallatai ayi Sallar Juma’a ba idan an bayar da Damar su su ci gaba da rufe masallatansu, kamar yadda suke son yi, saboda duk wanda Allah ya yi alkawarin zai mutu dalilin cutar Korona bairus sai ya mutu, hana shi fita domin zaman gida da ake kira Lockdown, ba zai hana mutum mutuwa ba”. Inji Sambo Rigachikun.
Ya dace Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi koyi da wasu Jihohin irin na makwabciyarta Jihar Neja, an ware ranaku uku ne a mako ranar Talata sai kuma ranakun Juma’a da Litinin da aka ba musulmi damar yin Sallar Juma’a saboda an ware daga karfe shida na safe har zuwa karfe 12 na dare haka ranar Lahadi daga shida na safe zuwa 12 na dare.
Sai kuma Jihar Kebbi ana yin Sallar jam’i ana Asham, ana Tarawihi kuma ana yin wa’azin Azumin wannan wata a ko’ina a Jihar.
Haka nan kamar yadda Malam Yusuf Sambo Rigachikun ya ce ” sun samu labarin cewa shima Gwamnan Gombe yana tattaunawa da Malamai na dukkan bangarori domin samun mafita game da halin da ake ciki.
A saboda haka ne Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce suke yin kira hade da  roko da abar su su samu damar aiwatar da Ibada domin ita ce ta fi masu komai a rayuwa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.