Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar kaduna ta bayyana cewa tana nan tana sa idanu a kan mutane uku da suka dawo Nijeriya daga kasar waje
Ma’aikatar lafiya ta Jihar Kaduna ce ta bayyana hakan a cikin wata takardar da aka aikewa manema labarai a kaduna
Kamar yadda suka bayyana cewa mutanen uku sun dawo ne daga kasar Ingila wato mutane biyu sai kuma wanda ya dawo daga kasar Egypt da a halin yanzu suke zaune su kadai.
Kamar yadda kwamishinar lafiya Dakta Amina Mohammed Baloni ta ce mutanen ya zuwa yanzu ba su nuna alamun cutar amma.duk da haka ana shawarartar jama’a da su kwantar da hankalinsa.
Duk wannan na kunshe ne a cikin wata takardar da kwamishiniyar Dakta Amina Baloni ta fitar a Jihar.
Ta bayar da tabbacin cewa cibiyar da aka tsara da kayan aiki a shirye take domin shirin kota kwana game da cutar Korona.
Takardar ta ci gaba da cewa Kwamishiniya Dakta Amina Mohammed Baloni sun tattauna da shugaban asibitin Gwamnatin koyarwa na Jiha na Barau Dikko sun kuma tattauna da asibitin koyarwa na Gwamnatin tarayya na jami’ar Ahmadu Bello da babban asibitin kunne da kuma wakilan asibitin idanu na kasa da ke kaduna domin tabbatar da aniyar kare lafiyar jama’a da aka Sanya a gaba.