Home / KUNGIYOYI / Muna Yin Ayyukan Gyaran Hanya Da Aljihunmu – Sakataren Direbobin Tifa Kwamared Musa Dan Hajiya

Muna Yin Ayyukan Gyaran Hanya Da Aljihunmu – Sakataren Direbobin Tifa Kwamared Musa Dan Hajiya

….An Karrama Kunguyar Direbobin Tifa A Jihar Kaduna

Daga Imrana Abdullahi

 Kwamared Musa Muhammad Dan Hajiya Sakatare ne na kungiyar direbobin Tifa a Jihar Kaduna ya bayyana cewa suna kokarin gudanar da gyare gyaren hanyoyi a cikin birane da kuma karkara musamman hanyoyin da suke yin amfani da su wajen dauko Yashi, Dutse ko kasa da ake yin amfani da su wajen ayyukan gine gine na yau da kullum.

Kwamred Musa Dan Hajiya ya shaidawa manema labarai hakan ne jim kadan bayan ya karbi lambar karramawa da hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen Jihar Kaduna ta ba su a matsayin kungiya baki daya.

Kwamared Dan Hajiya ya ci gaba da bayanin cewa sakamakon irin Namijin kokarin da suke yi ne a yau da kullum wajen gina kasa da tattalin arzikin ta ya sa wannan hukuma ta Gwannatin tarayya ta ga dacewar a ba su wannan lambar karramawa a kuma gagarumin taron da aka yi domin fadakar da jama’a muhimmancin kula da dokokin hanya a wadannan watanni hudu na karshen shekara da ake kira da watannin Emba.

“Jama’ar da suke a zaune cikin kauyuka sun san cewa muna yin iyakar kokarin mu wajen kulawa da hanyoyin da muke amfani da su wajen dauko kayan da muke kaiwa jama’a, Gwamnati, Kamfanoni da dai sauran dai daikun mutane ga duk wanda ke son a kawo masa a ko’ina yake. Shi yasa ma mutanen kauyukan da muke yin amfani da hanyoyin zuwa wurarensu ke maraba da masu sana’ar Tifa a koda yaushe”.

Kuma muna yin godiya da hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen Jihar Kaduna da ta ga dacewar a kwakulo mu a kuma Karrama mu hakika wannan abin alfahari ne a gare mu baki daya, saboda hakan zai sa mu kara yin kaimu ga sana’ar da muke yi ta direbancin Tifa duk da cewa daman can muna aiki tare da hukumar kiyaye hadurra ta kasa, wanda ba wai sai a karshen shekara ba a duk lokacin da za su yi wa jama’a wani taron karawa Juna sani sai sun gayyaci yayan kungiyar direbobin Tifa  domin a samu fadakarwar da ake yi a kan ababen hawa da da suka kunshi Keke Napep, Motoci da ita kanta Tifa da dai sauran ababen hawa wanda ko a hakan duk mun dauke shi a matsayin karramawa ne domin ana yi tare da mu”.

Dan Hajiya ya kara da cewa suna godiya da aka nuna lallai suna da amfani a cikin al’umma har aka ba su lambar karramawa da aka ba Kwamandan shiyya Malam Inusa Abdulkadir don haka ba wai shi kadai aka Karrama ba duk kungiyar ne baki daya kuma ba wai cikin garin Kaduna ba kawai akwai rassa a sauran wurare daban daban da suka hada da Zariya, birnin Gwari, Kafanchan duk sun kuma halarta kuma duk duniya za ta ga karramawar”.

” Koda yake wadansu mutane ba su fahimci ma me ake nufi da Tifa ba domin ita ba mota bace da ake tafiya yawo ko wata hira ba duk inda kaga Tifa kai ta aka yi. Kuma mutum ne ya bayar da kudinsa sannan aka kawo masa kayan da zai yi amfani da su son haka Tifa kenan a matsayin motar aiki.

Dan Hajiya ya kuma bayar da tabbacin cewa ko a shekarar da ta gabata sai da hukumar kiyaye hadurra ta kasa ta ga cancantar wannan kungiya ta direbobin Tifa da suje wurin dai dai Kofar shiga ta Kwamandan sojoji a Jaji kuma mun je mun kuma gyara wannan wuri duk da cewa hanya ce ta Gwamnatin tarayya amma mun yi wannan aiki domin an ga dacewarmu da muyi hakan, haka muka sayi kwalta da kudin mu muka kuma gyara wannan Ramin, saboda haka idan muna da kwarin Gwiwar zuwa irin wannan wuri mu kuma yi aikin gyara to, ina ga hanyoyin da muke amfani da su wajen dauko kaya?

“Kauyukan da muke zuwa dauko kaya zamu iya cewa ba su san Gwannati ba sai direbobin Tifa domin aikace aikacen da muke yi na hanya saboda da Damuna zaka ga hanyarsu ta lalace ba za su iya fita cin kasuwa ko kai amfanin Gona da dai sauransu ba amma wannan kungiyar sai ta gyara hanyar da ake bi a dauko Yashi. A yanzu haka muna yin alfahari da dukkan ayyukan da muke yi a cikin Jihar Kaduna

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.