Home / Labarai / Mutanen Hayin Banki Sun Koka Game Da Batun Gidajensu Da Wani Kamfani Ya Kai Kararsu
Executive Governor of Kaduna State Nasir El-Rufai speaks during an interview with Reuters in Kaduna, Nigeria November 1, 2016. REUTERS/Afolabi Sotunde - S1BEUKTKGYAA

Mutanen Hayin Banki Sun Koka Game Da Batun Gidajensu Da Wani Kamfani Ya Kai Kararsu

IMRANA ABDULLAHI KADUNA
Sakamakon karar da wani kamfani ya kai wadansu al’ummomin unguwar Hayin Banki inda yake karar wadansu mutane Tara da Coci guda uku ya sa lauyan mutanen kokawa ga manema labarai da bisa lamarin ga dai yadda, Lauya A M Imam, ya bayyana wani mutum da ke da kamfani ne ya kai karar wadansu mutane guda Tara, da Coci Coci na unguwar da kuma Ayarin wadansu mutane da ya kira da ba a Sani ba.
Lauya A M Imam ya ce dalilin da ya sa kenan mutanen da ake kara suka zo gaban kotu.
Sai dai su wadanda aka kai kara sun yi Ayarin jama’a da yawa da suka halarci kotun kamar dai yadda al’adar mutanen arewacin Najeriya take idan an yi karar mutum makwabcinsa kan bishi zuwa kotun domin nuna masa goyon baya.
Lauya A M Imam ya ci gaba da cewa dalilin zuwansu babbar  kotun Jihar Kaduna mai lamba ta 10 kenan, domin mai karar na neman kotun ta tabbatar masa da wasu rukunin gidaje a Unguwar Hayin Banki Kaduna kuma a yau ne shari’a ta fara.
Lauya ya ce ” kamar dai yadda kake gani harkar shari’a har yau ko shi wanda ke kara bai san adadin gidajen ba, amma mu iya sanin mu mun san ya kai kara na gidaje, Makaranta da Coci Coci guda uku da suka kama gidaje guda Takwas kenan, amma sai dai ya kira wasu mutanen da ba a san su ba a karar sa, wato a mutane na Tara da yake kara kuma su kansu mutanen ba su san adadinsu ba kamar yadda zaman kotu ya kasance ko shi bai san adadin mutanen ba sai lokacin da aka tantance ne za a san ko adadin gidaje nawa ne yake kara a kai sai dai alamu gidajen na da yawa”.
Haka kuma a game da yawan fadin filin, Lauya ya kara da cewa ya na daga cikin abin da za su kalubalanta a gaban kotu a irin wannan shari’a dole ne wadansu abubuwa su faru a yanayin ambaton kara, ” daga ciki har da adadin fadin murabba’in filaye a san yawan taku nawa ne da sauransu.
“Akwai kuma wadansu Kura kura kuran da aka yi na sa karar don haka ba mu son a sanar da wannan shi ya sa ba zamu fadi komai ba game da fadin wuri saboda muna da abin da za mu gaya wa kotu a kan wannan matsalar”.
Lauya ya ci gaba da cewa ya na fatan samun nasara a  kotu, wadannan yan uwana ne Talakawa da akasarinsu suna wurin shekaru 30, 40, 45 sun gina gidaje sun zauna a wurin kaga tun da ina wakiltarsu lallai ne in yi fatar mutumin da nake wakilta ya yi nasara, amma sauran wadan da ba a Sani ba za mu tantance su mu gani kuma a san adadin shekarun da kowa ya zauna a wurin domin muji wane
Wane ne mai zaman wurin shekaru 50 ko 70 a wurin zaune.
Mutanen da nake wakilta ina shawartar su da su zauna lafiya domin ana yin nasara ne idan akwai natsuwa da kwanciyar hankali ba tashin hankali ba, ina son kowa ya zama mai natsuwa da hadin kai manyansu su kwantar da hankalin yara na kasa da su tun da magana na kotu a saurari abin da kotu za ta yi.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.