Home / Idon Mikiya / Mutuwar aure da kutsen zamani a zamantakewar ma’aurata

Mutuwar aure da kutsen zamani a zamantakewar ma’aurata

RA’AYI

 

Daga Yusuf Dingyadi

 

Daya daga cikin muhimman dalilan mutuwar aure a kasar Hausa da wasu masu nazari ke gani na yawaita a cikin wannan zamani akwai mummunar dabi’ar da aka cusa ma wasu matan aure dangane da yin fito na fito da mazajensu; ci gaba da zargin mazaje na tauye ma mata hakkokinsu, mussaman a kan nuna musu kada su zama tamkar bayin mazajensu kan irin tarbiyyar da zamantakewa da akeyi a baya, har suke daukar zuga daga wasu fina-finan hausa da kungiyoyin kare hakkokin mata na tabbatar musu da cewa, lokaci ya yi ga mata na su nuna suna da YANCI!

 

Wata matsalar har da lalacewar tarbiyya da karancin fahimtar addini da sanin hanyoyin inganta hakkokin aure da kutse a kan wayewar zamani da mafi rinjayen mata wadanda suke ganin ala dole NAMIJI yana tauye hakkin matarsa.

 

Mafi rinjayen masu yada wadanan manufofin a cikin al’umma, har suna kara yi wa mata mugunyar huduba na mutuwar aure da samun rashin fahimta; sune wasu matan da suka rayu a kan kasa zaman aure ko wayewa da wayo ya hana su auren don yadda suke ganin  namiji bai Isa ya tankwasa su ba, saboda zurfi a cikin al’adun turawa da na zamani da ke ganin zaman aure tamkar ra’ayi ne ba IBADA ba.

 

Wadanan ne da wasu makamantansu  da suka mayar da kankantar sabanin zamantakewa ta aure a matsayin hujja ga cin zarafi mazajensu, har suke kara janyo mutuwar aure da rarrabuwa da yawaitar ZAWARAWA a cikin al’umma saboda suna ganin Namiji a matsayin BUTULU wanda ake iya cin amanarsa kamin yaci tasu!!!

Ko minene MAFITA?

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.