Home / Lafiya / Na Gano Maganin Korona Bairus – Forofesa Ayodele 

Na Gano Maganin Korona Bairus – Forofesa Ayodele 

Furofesa Ayodele Israel Adeleye daga Jihar Kaduna a tarayyar Nijeriya ya bayyana cewa ya gano maganin kwayar cutar Covid – 19 da ake kira Korona da ta addabi duniya a halin yanzu.
Furodesa Ayodele ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a kaduna inda ya sha alwashin cewa yana son Gwamnati ta bashi mutane biyar da zai yi wa maganin cutar Korona birus kyauta domin a tantance gaskiyar maganinsa.
Ya kuma shaidawa manema labarai cewa maganin da ya gano zai magance suk wata matsalar da ake fama da ita a kan wannan kwayar cuta ciki har da batun rufe jama’a cikin gidaje sakamakon hana su fita.
 Furofesa Ayodele Israel Adeleye wanda ya kasance a kan gaba wajen bincike da a kan kimiyyar fasahar Gwaje gwaje ya tabbatarwa da manema labarai cewa a shirye yake ya warkar da mutane biyar da ke da cutar Korona Bairus kyauta domin ya fayyace gaskiyar maganinsa da yake bayani a kansa saboda yan Nijeriya da duniya baki daya.
Furofesa Adeleye wanda ya kasance tsohon Malami ne a jami’ar Ahmadu Bello kuma tsohon ma’aikaci a Asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, yana kira ga daukacin jami’an Gwamnati a dukkan mataki da kuma masu ruwa da tsaki a kan harkar lafiya da kada su yi kasa a Gwiwa wajen jaraba wannan maganin nasa domin amfanin al’umma, kasancewar cutar Covid – 19 da ake kira da Korona bairus na yin Illa ga ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.

About andiya

Check Also

Gwamnatin Hadin Kan Jama’a Na Haifar Mana Da Nasara – Gwamna Uba Sani

  …Nan da Sati biyu za a fara aikin garin Tudun biri Daga Imrana Abdullahi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.