Related Articles
A lokacin tafiye-tafiyen aiki da na yi a cikin ‘yan kwanakkin nan, na yi mu’amular aiki ta qut-da-qut da wasu manyan mutane wadanda gwajin da aka gudanar ya nuna sun harbu da cutar Korona (Covid-19) a saboda haka Likitoci sun ba ni shawarar in ke6e kaina da ga jama’a.
A saboda wannan daga yau Jumu’a 18/12/2020 na janye kaina da ga gudanar duk wani aiki da zai wajabta cudanya da jama’a har sai na cika wa’adin da ka’idar kariyar cutar Korona (Covid-19) ta tanada.
A duk tsawon wannan lokaci Mataimaki na, Honarabul Manir Muhammad Dan’Iya (Walin Sokoto), Shi ne zai gudanar da ayukkan Gwamnatin Jahar nan kamar yadda kundin tsarin mulki na kasa ya tanada.
Yanzu zan mayar da hankali ne ga gudanar da gwaje-gwajen da ake bukata a irin wannan yanayin kamar yadda kwamitin yaki da cutar Korona Covid-19 na jaha da Hukumar binciken cututtuka ta kasa NCDC da kuma Hukumar lafiya ta duniya sun ka shata.
Ina Kuma rokon ku addu’a, Allah Ya albarkaci Al’ummar Jahar sokoto da Najeriya baki-daya.
Wadannan bayanai dai sun fito ne daga babban mai magana da yawun Gwamnan Jihar Sakkwato Muhammadu Bello da ya rabawa manema labarai.