Home / Labarai / An Saki Dukkan Daliban Makarantar Kankara – Masari

An Saki Dukkan Daliban Makarantar Kankara – Masari

An Saki Dukkan Daliban Makarantar Kankara – Masari

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa an saki baki dayan Daliban da aka kwashe daga makarantar sakandare ta garin Kankara cikin Jihar Katsina.
Gwamna Masari ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da kafar yada labarai ta gidan Talbijin na kasa NTA da aka yada kai tsaye ta na’urar manhajar zoom da aka yada da karfe 9 na Daren yau Alhamis
Gwamna Masari ya ci gaba da cewa suna nan suna shirye shiryen duba lafiyarsu domin hada kowa da iyayensa.
Gwamnan ya ce domin gujewa faruwar irin abin da ya faru a makarantar sakandare ta Kankara a halin yanzu za su yi amfani da wadansu Yan Sanda na musamman tare da wadansu jami’an tsaro na kasa da kuma wadansu mutanen da suka kasance makwabtan makarantun da za su taimaka wa jami’an tsaro a samu ingantaccen tsaro a kowace makaranta.
Gwamna Masari ya ci gaba da bayanin cewa sun dauki matakin tabbatar da tsare dukkan inda aka ajiye Daliban nan a cikin dajin da suke kuma sun umarci jami’an tsaron da suka zagaye wurin da kada su yi harbi ko daya domin a samu nasarar kubutar da yaran ba tare da an samu ko kwarzane ba, kuma hakan ta faru, ” muna godiya ga Allah”.
Muna dai godiya ga dukkan jama’ar duniya baki daya da suka yi ta addu’o’I domin kubutar da Daliban nan daga hannun wadanda suka kwashe su.

About andiya

Check Also

Gwamnatin Hadin Kan Jama’a Na Haifar Mana Da Nasara – Gwamna Uba Sani

  …Nan da Sati biyu za a fara aikin garin Tudun biri Daga Imrana Abdullahi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.