Home / Lafiya / NA KEBE KAINA – Inji Gwamna Jihar Sakkwato

NA KEBE KAINA – Inji Gwamna Jihar Sakkwato

NA KEBE KAINA….Gwamnan Jahar Sakkwato, Alahaji Aminu Waziri Tambuwal (CFR, Mutawallen Sokoto)

A lokacin tafiye-tafiyen aiki da na yi a cikin ‘yan kwanakkin nan, na  yi mu’amular aiki ta qut-da-qut da wasu manyan mutane wadanda gwajin da aka gudanar ya nuna sun harbu da cutar Korona (Covid-19) a saboda haka Likitoci sun ba ni shawarar in ke6e kaina da ga jama’a.

A saboda wannan daga yau Jumu’a 18/12/2020 na janye kaina da ga gudanar duk wani aiki da zai wajabta cudanya da jama’a har sai na cika wa’adin da ka’idar kariyar cutar Korona (Covid-19)  ta tanada.

A duk tsawon wannan lokaci Mataimaki na, Honarabul  Manir Muhammad Dan’Iya (Walin Sokoto), Shi ne zai gudanar da ayukkan Gwamnatin Jahar nan kamar yadda kundin tsarin mulki na kasa ya tanada.

Yanzu zan mayar da hankali ne ga gudanar da gwaje-gwajen da ake bukata a irin wannan yanayin kamar yadda kwamitin yaki da cutar Korona Covid-19 na jaha da Hukumar binciken cututtuka  ta kasa NCDC da kuma Hukumar lafiya ta duniya sun ka shata.

Kuma da sannu zan sanar da ku duk sakamakon binciken.Anan zan so in yi amfani da wannan damar in nanata kira ga jama’ar wannan jaha da mu ci gaba da bi sau-da-kafa duk sharuddan kare kai daga wannan cutar kamar yadda hukumomin lafiya zuka zayyana.

Ina Kuma rokon ku addu’a, Allah Ya albarkaci Al’ummar Jahar sokoto da Najeriya baki-daya.

Wadannan bayanai dai sun fito ne daga babban mai magana da yawun Gwamnan Jihar Sakkwato Muhammadu Bello da ya rabawa manema labarai.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.