Home / Labarai / Na Shiga Damuwa Da Kaluwa A kan Rushewar Masallacin Zariya – Kakakin Majalisar Tajudeen Abbas

Na Shiga Damuwa Da Kaluwa A kan Rushewar Masallacin Zariya – Kakakin Majalisar Tajudeen Abbas

Daga Imrana Abdullahi

addu’a ga wadanda abin ya shafa

…ya bukaci daukar mataki don hana sake faruwa

Kakakin majalisar wakilai  Honarabul Dokta Abbas Tajudeen,  ya bayyana rugujewar wasu sassa na babban masallacin Zariya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu a matsayin abin takaici da ban tausayi.

Kakakin Majalisar, Abbas wanda ke wakiltar mazabar Zariya ta Jihar Kaduna, ya ce ya samu labarin faruwar lamarin cikin kaduwa, inda ya ce ya yi matukar bakin ciki da mutuwa da raunata al’ummar mazabarsa a wannan lamarin.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Musa Abdullahi Krishi ya rabawa manema labarai.

shugaban majalisar ya ce “zuciyarsa ta yi jini ainun sakamakon faruwar lamarin, inda ya ce wannan shi ne labari mai ratsa zuciya da ya samu a ‘yan kwanakin nan.

Kakakin majalisar Abbas Teejuddeen, wanda ya bayyana alhininsa da alhinin asarar da aka samu a wannan mawuyacin lokaci, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.  Haka nan kuma ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da ya ba wadanda suka samu raunuka a lokacin da lamarin ya faru cikin gaggawa ya samu sauki.

“Zuciyata ta yi bacin rai game da abin takaicin da ya faru a babban Masallacin Zariya a ranar Juma’a 11 ga watan Agusta, 2023 a lokacin Sallar La’asar, a lokacin da wasu sassan masallacin suka ruguje, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu da ke Sallar La’asar.

“Abin takaici ne da ban takaici yadda mutanen da suka je bautar Allah suka rasa rayukansu a haka, ina rokon Allah madaukakin Sarki Ya ba su lafiya ya kuma saka musu da gudan Al’Jannatul Firdausi.

“Tunanina da addu’o’i na suna tare da iyalansu da kuma wadanda suka samu raunuka yayin faruwar lamarin.

“Ina mika sakon ta’aziyyata ga Mai Martaba Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, da al’ummar Zaria, da daukacin al’ummar Jihar Kaduna da ma Gwamnatin Jihar Kaduna bisa wannan mummunan lamari.

“Ina addu’ar Allah madaukakin Sarki ya baiwa iyalan wadanda suka rasa rayukansu ikon jurewa asara tare da samun saukin wadanda suka samu raunuka a lokacin faruwar lamarin.” Inji Shugaban Majalisar.

Ya kuma bukaci hukumomin da abin ya shafa a jihar Kaduna da su binciki lamarin da ya kai ga rugujewar sassan babban masallacin Zariya da nufin dakile afkuwar lamarin a ko’ina a jihar.

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.