Home / Labarai / Naira Miliyan 4.5 Ne Kudin Ajiyar Aikin Hajjin Badi

Naira Miliyan 4.5 Ne Kudin Ajiyar Aikin Hajjin Badi

Daga Imrana Andullahi

Hukumar Alhazai ta tarayyar Najeriya ta sanar da kudin ajiya ga masu niyyar zuwa aikin Hajjin badi da suka kai naira miliyan Hudu da rabi (4.5) da maniyyaci sai iya biya a asusun gata da ake ajiye kudin kafin sanar da ainihin kudin da za a biya a badi idan Allah ya kai mu shekarar 2024.

Kamar yadda wakilinmu ya ga wata sanarwa da ke yawo a kafafen yada labarai musamman na jaridun da ake wallafawa a yanar Gizo cewa an sanar da batun kudin ajiya ga masu niyyar zuwa aikin Hajjin badi 2024 da wakilinmu yaga sanarwar yawan kudin da suka kai naira miliyan hudu da rabi (4.5) nan da nan sai wakilin mu ya tuntubi jami’an yada labaran hukumar ta hanyar yin amfani da dandalin Sada zumunta na whatsapp, inda kuma mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara, ta tabbatar da cewa hakika haka sanarwar take wato gaskiya ce.

“Amma dai ya zuwa yanzu ba a sanar da ainihin hakikanin kudin da Za’a biya ba na kudin kujerar aikin Hajjin badi wato shekarar 2024 sai dai wannan miliyan hudu da rabi an dai fadi kudin asusun ajiya ne kawai ga masu son biyan kudin aikin Hajji na badi. Ba a dai ce haka kudin yake ba ko zai iya yin kasa ko sama da hakan har yanzu ba a tabbatar ba tukuna”, kamar yadda mai magana da yawun hukumar aikin Hajjin ta aike domin amsa tambayar da wakilin mu ya gabatar.

Gaskiya ne “Amma ba’a tabbatar cewa zai tsaya a hakan ko zai fi ko ya yi kasa ba tukunan. Wannan kudin asusu ne kafin tabbatar da ko nawa ne iya adadin kudin hajjin”, kamar yadda Fatima Sanda Usara, ta rubuta a dandalin.

Sai dai karin hasken da muka samu daga Malam Shu’aibi, da shima ya amsa tambayar batun kudin asusun ajiya ne miliyan 4.5 cewa ya yi.

Kamar yadda ya rubuta a dandalin Sada zumunta na whatsapp yanar Gizo a dandali mai suna NAHCON infor center 2;

“Eh haka ne ɗan uwa.

Duk maniyyaci zai fara ajiye Miliyan 4.5.

Idan akwai ƙari za a yi bayani sai ya cika”.

Idan kuma an sami ragi za a dawo masa da canji in sha Allah.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.