Mustapha Imrana Abdullahi
Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu ya bayyana Noma a matsayin sahihiyar hanya ingantatta wadda za ta ciyar da tattalin arzikin Najeriya gaba.
Alh Mannir Yakubu ya kuma bayyana nasarori da ci gaban da gwamnatin jihar katsina ta samu a fannin noma a jihar Katsina a wurin taron shekara shekara da gidauniyar tunawa da Sa, Ahmadu Bello Sardauna ta shirya a dakin taro na gidauniyar da ke Kaduna.
Alhaji Mannir Yakubu ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatin jihar katsina da suka bada da samar da tarakatoci, wadataccen takin zamani bisa farashi mai sauki da irrai da sauran kayan da ayyukan gona ke bukata domin habbaka harkokin noma ajihar Katsina.
Mataimakin gwamnan ya bayyana Jihar Katsina jihar dake gaba gaba wajen noma abinci mai yawa da arewacin kasar ke amfani da Shi tare da sauran kayan da noma ke samarwa.
A nashi jawabin Shugaban kwamitin amintattun gidauniyar tunawa da sir Ahmadu Sardaunn Sokoto tsohon gwamnan jihar neja Alhaji mu’azu babangida Aliyu yace gidauniyar an kafa ta ne domin cigaban arewacin najeriya da najeriya baki daya, wato dasawa daga wurin da sir’ Ahmadu sardauna ya tsaya.
Bayan kammala taron rana. An gudanar da walimar cin abinci da yamma tare da karrama wasu mutane da suka bada gagarumar gudummuwa wurin ci gaban arewacin najeriya da kasa baki daya.