Home / News / Nasarar Ganduje Ta Al’umace – Honarabul Gwarzo

Nasarar Ganduje Ta Al’umace – Honarabul Gwarzo

Daga Imrana Abdullahi
An bayyana nasarar da Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samu a matsayin nasarar al’umma baki daya.
Duba da irin yadda Jihar Kano ta zama Jihar daukacin al’ummar duniya ce baki daya kasancewar kowa na gudanar da hada hadar kasuwanci a cikin Jihar.
Shugaban hukumar tsaftace muhalli na Jihar Kano Honarabul  Abdullahi M Gwarzo ne Ya Bayyana hakan a Zantawarsa Da manema labarai Jim Kadan Bayan Kammal shariar Da Jamiyyar PDP ta Shigar tana Kalubalantar Nasarar Dakta Abdullahi Umar Ganduje a zaben Gwamnan da ya gabata.
Ya ce hakika dolene ayi wa Allah godiya domin Wannan Nasarace ta Jama’ar Kano da kuma  malaman Kano duba da irin yadda yake yi wa addini da mutanen Kano arewacin kasa da kasar baki daya hidima baki daya.
Ya kuma ci gaba da cewa ya zama wajibi ga dàn Jamiyyar APC na Jihar Kano ya kara daura damara domin tunkarar ragowar kalubalen da ke gabanmu Wato mu zama tsintsiya madaurinki daya.
Ya kuma kara Kira g masu rike da mukamai a jahar da su dubi Allah su taiimaki yan Jamiyyar da ke fadin Jihar Kano domin acewarsa matasa sun bada gudunmuwa musamman a kan zaben Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Jamiyyar APC tun daga sama har kasa baki daya.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.