NUJ Kaduna Ta Karrama Kwamishina Ahmad Mai Yaki Da Lambar Yabo
Daga Imrana Abdullahi
Sakamakon kokari da aiki tukuru domin ganin aikin jarida tare da Samar da kyakkyawar dangantaka tsakanin Gwannatin Jihar Kaduna da kuma daukacin Yan jaridu da suke gudanar da aikinsu na yada bayanai an samu fahimta da ci gaban Jihar Kaduna tare da kasa Baki daya.

Hakan ta Sanya kungiyar Yan jarida ta kasa NUJ reshen Jihar Kaduna ta duba irin kwazon Kwamishinan ma’aikatar yada labarai ta Jihar Kaduna Alhaji Ahmad Mai yaki ya samu kyakkyawar Lambar karramawa a wajen Babban Taron kungiyar NUJ Kaduna na karshen shekarar 2025.

A wajen wannan taron karshen shekara na NUJ Alhaji Yunusa Muhammad ne ya wakilci Kwamishinan yada labarai na Jihar Kaduna inda ya karbi lambar shaidar karramawar a madadin Kwamishinan Ahmad Mai yaki.

A wajen Taron dai an kuma karrama wakilan kafofin yada labarai da suke aikin a cikin garin Kaduna da Jihar Baki daya da nufin a Kara karfafa masu kwarin gwuiwar gudanar da aikin kamar yadda ya dace.
Kwamared Garba Muhammad tsohon shugaban kungiyar NUJ reshen Jihar Kaduna kuma tsohon amintaccen kungiyar a matakin kasa ne ya mikawa Kwamishina Ahmad Mai yaki Lambar karramawar ga wakilin Kwamishina Yunusa Makarfi.

THESHIELD Garkuwa