Home / Big News / PDP Ce Jam’iyya Da Gwamnatin Da Ke Mutunta Al’ummar Kasa – Mazawajen Bakori

PDP Ce Jam’iyya Da Gwamnatin Da Ke Mutunta Al’ummar Kasa – Mazawajen Bakori

Daga Imrana Abdullahi
An bayyana jam’iyyar PDP a matsayin wadda ta kafa Gwamnatin da ke gani da mutunta al’ummar kasa baki daya.
Honarabul Aminu Magaji, Mazawajen Bakori tsohon shugaban karamar hukumar Bakori da ke Jihar Katsina ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da wakilin mu ta wayar tarho.
Honarabul Mazawaje ya ci gaba da bayanin cewa kamar yadda kowa ya sani a lokacin Gwamnatin PDP ne aka samu walwala da samun duk wata damar da hatta talakawan kasa sun shaida ana yi da su, don haka PDP ce jam’iyyar da har yanzu kowa ya amince da ita.
“Talakawa da dukkan sauran jama’a na cikin kasa wadanda suka isa jefa kuri’a da wadanda ba su ma isa yin zaɓe ba kowa na son PDP, saboda haka muma muna nan a cikinta.
Sai ya kara da cewa amma matsalar kawai da PDP ke fuskanta ita ce daga can sama inda aka kaka ba Wike ya na abin da yake so, don haka muna nan cikinta in an samu an gyara daga sama shikenan mun san dai a can kasa Talakawa na son PDP domin ta daraja su ta martaba su sun kuma samu alkairi da ci gaba a dukkan al’amuran su na rayuwa ba kamar yadda ake a yanzu ba.
Kamar yadda muka fahimta ,” Mu da muka yi wa jama’a jagoranci mun san yadda abin yake kuma a halin yanzu mun ga cewa sai dai zaɓaɓɓe kawai ko kuma wanda ke kusa da wadanda aka zaba din kawai suke iya duk wata walwala, amma sauran jama’a sun koma yan rabbana ka wadata mu kawai,don haka PDP ce mafita sai dai idan mun ga lamarin yadda ya kasance shikenan,amma a yanzu muna nan cikin PDP ba ja da baya sai abin da ya turewa Buzu Nadi”.

About andiya

Check Also

Cloves farming pilot in Nigeria is significantly gaining Momentum.

By; Imrana Abdullahi Members of the Cloves Producers, Processors, and Marketers Association in Nigeria paid …

Leave a Reply

Your email address will not be published.