Home / News / PDP TA SAMU KOMA BAYA A JIHAR SAKKWATO 

PDP TA SAMU KOMA BAYA A JIHAR SAKKWATO 

Sakamakon irin yadda al’amura suka zamar wa jam’iyyar PDP koma baya ya haifarwa shugabannin Yakin neman zaben Ubandoma/ Sagir Network barin jam’iyyar zuwa APC
Sun bayyana jam’iyyar PDP a matsayin mara alkibla da babu makoma.
Yan kwanaki da suka rage a fara fafutukar gangamin Yakin neman zaben Gwamna na shekarar 2023 a tarayyar Najeriya, sai kawai a Jihar Sakkwato ga shugabannin kungiyoyin da ke tallafa wa dan takarar Gwamnan Jihar Sakkwato, Ubandoma/ Sagir Network a karkashin jam’iyyar PDP, Malam Sa’idu Umar Ubandoma ya fice daga jam’iyyar zuwa APC.
Shugaban tawagar, da suka canza shekar daga PDP zuwa APC, Alhaji Ahmad Labaran, tare da sama da  mutane  300 da suka hada da Maza da Mata na yayan kungiyar, ya ce sakamakon rashin ingantaccen tsarin siyasa ne ya sa suka yanke hukuncin ficewa daga PDP zuwa APC domin samun yin aiki da masu ingantaccen tsarin da kowa zai yi alfahari da shi sakamakon samun mafita.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun
Bashar Abubakar, mai bayar da shawara na musamman a kan harkokin kafofin yada labarai ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko
Labaran ya ci gaba da cewa ya yi da na sanin kasancewa dan jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato,ya kara da cewa lokacin da ya bata a PDP da ya Sani ya yi amfani da wannan lokacin ya taimaki kansa idan ya kasance a cikin jam’iyyar APC.
Ya shaidawa taron jama’ar cewa zai yi wa jam’iyyar APC aiki ta hanyar fadakar da jama’a su bayar da hadin kai da goyon bayansu wajen samun nasarar zaben 2023 mai zuwa.
Da yake karbar wadanda suka canza shekar a madadin shugaba kuma jagoran jam’iyyar APC,  Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, shugaban jam’iyyar APC na Jihar Sakkwato, Honarabul Isah Sadiq Achida tabbaci ya ba wadanda suka canza shekar cewa za a rika tafiya da su kamar komawane dan jam’iyyar APC.
Ya kuma jaddada cewa, idan aka zabi jam’iyyar APC ta dare kan karagar mulki a Jihar, hakika jam’iyyar za ta tabbatar da yi wa kowa adalci tare da dai- daito ga kowa domin samun ciyar da Jihar Gaba.
Achida ya kara da cewa, Gwamnatin APC a Jihar za ta inganta da bunkasa harkokin masu kanana da matsakaitan sana’o’i da kuma Farfado da dukkan fannonin da duka durkushe a mulkin PDP a Jihar Sakkwato.
Dan takarar Gwamnan na APC a Jihar Sakkwato Honarabul Ahmad aliyu Sakkwato, wanda tsohon kwamishina kuma jigo a jam’iyyar APC a Jihar, Honarabul Muhammad Tukur Alkali, yayin da yake mataba da wadanda suka canza shekar zuwa APC ba su tabbaci ya yi cewa ba za su yi Dana sanin komawarsu cikin APC ba domin jam’iyyar a shirye take ta karbi karin wadansu magoya bayan PDP zuwa APC kuma dukkan yayan jam’iyyar za a ta fi tare da Juna babu wani bambanci.
Tukur Alkali, ya bayar da tarihin can baya a zamanin Gwambatin Wamakko, inda yake cewa tallafa wa matasa na daya daga cikin abubuwan da ake ba muhimmanci a Gwamnatin da ta ba dimbin matasa ayyukan yi.
Sai ya bayar da tabbacin cewa, idan har Ahmad Aliyu ya zama Gwamnan Jihar Sakkwato, sai Farfado da ayyukan da aka yi watsi da su a lokacin mulkin Tambuwal domin kara inganta rayuwar jama’a, wanda shi ne manufar Gwamnatin APC.
Hakazalika a wajen taron wata cibiyar bayar da tallafi ga jama’a mai suna “A’isha Foundation” sun tallafa wa muta sama da dari da taimakon kudi a lokacin taron.
Taron wanda aka yi a Unguwar Malamai, da ke yankin karamar hukumar Sakkwato ta Kudu ya samu halartar mutane kamar haka, dan majalisar wakilai ta kasa Honarabul Almustapha Abdullahi Dust, yan takarar majalisar wakilai da majalisar Jiha, Honarabul Bala Hassan Abubakar III, da Alhaji Aminu Gidado Jegawa.
Sauran sun hada da Sakataren jam’iyyar APC na Jiha, Abubakar Muhammad Yabo,ma’ajin jam’iyyar Haruna Adiya, jami’in yada labarai na jam’iyyar Sambo Bello Danchadi, tsofaffin shugabannin karamar hukumar Sakkwato ta KuduHonarabul Ya’u Muhammad Danda da Honarabul Aminu Sani Liman da dai sauran jama’a da dama.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.