Mustapha Imrana Abdullahi
Mataimakin shugaban jam’iyyar PRP reshen Jihar Kaduna St Kamvem Nannim ya yi kira ga daukacin yan Nijeriya da su rungumi jam’iyyar PRP domin ita ce kadai ta ragewa Talakawan kasar domin samun tsiran da zai tabbatar da ingantacciyar nasara.
St Kamvem ya bayyana wa manema labarai a Kaduna cewa bayanin hakan ya zama wajibi kasancewar yan Nijeriya sun san halin da kasar suke ciki a kan fannoni daban daban.
” Dukkan talakawan Nijeriya ya dace su dawo daga Rakiyar duk wani ko gungun wadansu mutane da duka san irin takun sa ko ta halayya ko kuma ta hanyar gudanar da mulki domin tantancewa kafin lokacin da za su ce ga wanda za su Sanya a gaba”.
Ya ci gaba da cewa ” yayan jam’iyyar PRP ba za su yi kasa a Gwiwa ba wajen ganin sun kaucewa wasu mutanen da a lokutan zaben baya da suka gabata aka tabbatar da cewa su na yi wa wata jam’iyya aiki ne da sunan PRP, hakika hakan ba za ta faru ba”, inji shi.
” za mu shiga zaben kananan hukumomin da za a yi a Jihar Kaduna kuma muna tabbatar wa da jama’a cewa dukkan abin da hukumar zabe ta Jihar Kaduna take aiwatarwa ta na aikowa ainihin jam’iyyar PRP kuma muna halarta domin mune yayan PRP sahihai da aka Sani da ke aiki tukuru domin ganin PRP ta samu nasara a dukkan matakan zaben da za a gudanar”.
A game da irin yadda wani bangare ya aiko da takardar ayi taron samar da shugabanni na Jiha kuwa, Kamvem ya ci gaba da cewa ya dace idan wannan takardar da shirin da ake kokarin yi na gaskiya ne ya dace a aiko takarda zuwa ga shugabanni da ofishin PRP na Jiha domin a aikewa sauran rassa tun daga mazabu zuwa yankunan Jiha domin aiwatar da abin da ya dace, amma kokarin a aiwatar da wani abu daga can sama kuma a Jiha bayan ga mu a matsayin shugabanni na Jiha, haba wannan abu ai ba wanda zai amince da shi.
Ya kuma yi kira ga shugabanni da daukacin yayan PRP na Jihar kaduna da kasa baki daya da su ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukan da za su ciyar da PRP da kasa baki daya gaba kuma nan gaba kadan za a samu tabbataccen hukuncin kotu game da shari’ar da ke gaban kotun Gwamnatin tarayya, wanda hakan zai taimaka wa kowa a samu ciyar da kasa gaba.
Ya kara yin kira ga yayan PRP cewa su ci gaba da natsuwa musamman idan sun ji wata sanarwa su tabbatar sun tantance ta daga ina take domin gujewa masu yin amfani da sunan PRP a cimma wata bukata da kashin kai.