Home / Labarai / RASHIN KISHIN KASA KE HAIFAR DA KASHE KASHE, SATAR JAMA’A  – DAN MARAYAN ZAKI

RASHIN KISHIN KASA KE HAIFAR DA KASHE KASHE, SATAR JAMA’A  – DAN MARAYAN ZAKI

DAGA IMRANA ABDULLAHI

AN Bayyana matsalar rashin kishin kasa da cewa shi ne ke haifar da matsalar tsaron da ta kai ga Satar jama’a da kashe kashe a Najeriya.

Honarabul Aliyu Muhammad Waziri, da ake yi wa lakabi da Dan marayan Zaki kuma Santurakin Tudun Wada Kaduna ne ya bayyana hakan a cikin wata tattaunawar da ya yi da kafar Talbijin ta DITV da ke Kaduna.

Aliyu Muhammad Waziri ya ce koda ana kashe mutum ya dawo a kuma kashe mutum ya dawo idan aka tambaye shi ina ya fi so zai ce Najeriya domin bashi da wata kasar da ta fi ta ko kadan.

” Ko me za ta zama nan ce kasa ta ba inda zan je, amma dai ba mu son komai ya ci gaba da faruwa na bacin rai da duk wani abu mara dadi a kasar nan, kuma ko muna so ko ba ma so masu aikata wannan aikin yan uwan mu ne, yan kasar ne kuma yayan kasar suke yi wa wannan wanda bai kamata su aikata hakan ba”.

Dan marayan Zaki ya kara da cewa na farko dai babu inda aka bayar da wata dama ta wani ya ci mutunci ko zarafin wani balantana ya keta masa haddi, domin ana kama manya, yara maza da mata har da na goye da na hannu da kuma mai ciki duk an samu irin wannan har wasu matan na haihuwa a hannunsu. Kuma wani misali duk abin da  mutum komai takamarsa Mace ta haife shi duk girmansa duk rawaninsa, saboda haka cikin mace abu ne mai dimbin tarihi da ya fitar da Annabawa, Malamai, Alkalai, shugabannin da makaranta wato masana da dama, har da masu hankali da sabanin hakan amma ba wadda take son ta haifi dan ta ya zama a cikin wadancan mutanen”. Inji dan marayan Zaki.

Sai ya kawo hankalin jama’a da kada su sake a rika yin zama irin na al’ummar Shedan da aka yi a can baya inda wancan zuri’a za ta tashi ta kashe waccan wannan ta kashe waccan haka kawai.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.