Home / Labarai / SARDAUNAN FUNTUWA ALHAJI AKILU HASSAN YA YI KIRA GA AL’UMMA SU TASHI TSAYE WAJEN YIN ADDU’O’I

SARDAUNAN FUNTUWA ALHAJI AKILU HASSAN YA YI KIRA GA AL’UMMA SU TASHI TSAYE WAJEN YIN ADDU’O’I

Daga Abdullahi Sheme

 Alhaji Akilu Babaye Daraktan kamfanin rukunin NAK kuma Sardaunan sarkin Maskan katsina hakimin funtuwa da ke jahar katsina ya yi kira ga dukkan jama’ar kasar nan musamman na karamar hukumar funtuwa dasu dage da addioi domin samun zaman lafiya da Damina mai albarka.
Ya yi wannan kiran ne jim kadan da kammala nadinsa na sardaunan funtuwa a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadarshi dake garin funtuwa
   Alhaji Akilu Hassan ya godewa mai girma sarkin maskan katsina hakimin funtuwa wajen basu wadannan sarautu shida sauran ‘yan uwanshi wannan abin a yabane da kuma jindadi kuma babu shakka zasu kara jajircewa wajen nunka kokarinsu na kara kawo cigaba a jahar katsina musammam a karamar hukumar mulki ta funtuwa dama kasa baki daya.
  Sardaunan yacigaba da cewar yakamata matasan kasar nan sutashi tsaye wajen rungumar sana’o’in hannu ganin yadda Gwamnati bata iya samarma matasan kasar nan aiyukan yi Alhaji Akilu yace ba shakka kamfaninsu yana bada gagarumin gudunmawa wajen ba matasan jahar sanar yi kuma a shirye suke dasu cigaba da kara rungumar matasan wajen sucigaba da dogaro da kansu ya kuma kara nuna tabbacinshi akan gudunmawar da sauran ‘yan uwanshi da aka nadasu tare suke bayarwa don cigaban karamar hukumar funtuwa ako da yaushe kuma yanzune zasu kara nunka abin don cigaban yankin dama jaha baki daya yakuma nuna godiyarshi ga mai martaba sarkin katsina Alhaji Abdulmimini kabir usman wajen amincewarshi domin basu wadannan sarautu masu albarka da tarihi.
 A nashi jawabin godiyar Danmaliki Babba Alhaji kabir Bilya shima yakara nuna jin dadinshi da nuna godiyarsu ga maigirma sarkin maska da kuma nuna tabbacinshi wajen cigaba da bada gudunmawar wajen ciyar da yankin gaba kamar yadda suka saba sannan zasu cigaba da kara hada kawunansu da sauran ‘yan uwansu da aka nadasu tare wajen kara ba sarkin maska shawarwari masu kyau kamar yadda yake yi da ciyar da yankin gaba insha Allahu yakuma yabawa mai girma Gwamnan jahar Alhaji Aminu Bello masari wajen kokarinshi wajen gudanar da aiyukan cigaba a yankin musamman a fadin jahar sannan yayi kira ga Gwamnatin Tarayya data kawo karshen rashin tsaron daya addabi arewacin kasar nan musamman jahar katsina da karamar hukumarmu ta funtuwa a taimakamana asami saukin wannan matsalar ya godema dukkan al’ummar da suka sami damar halartar wannan gagarumin bikin nadin da akayi masu da fatan kowa yakoma gidanshi lafiya

About andiya

Check Also

Gwamnatin Hadin Kan Jama’a Na Haifar Mana Da Nasara – Gwamna Uba Sani

  …Nan da Sati biyu za a fara aikin garin Tudun biri Daga Imrana Abdullahi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.