Home / Labarai / Rundunar Yan Sanda Ta Kama Barayin Mota Biyu (2)

Rundunar Yan Sanda Ta Kama Barayin Mota Biyu (2)

Rundunar Yan Sanda Ta Kama Barayin Mota Biyu (2)
Mustapha Imrana Abdullahi
Rundunar Yan Sanda ta kasa reshen Jihar Kaduna karkashin jagorancin kwamishinan yan Sanda UM Muri ta bayyana cewa ta samu nasarar kama wadansu da ake yi wa zargi da satar motoci biyu.
Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwar da ke dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar ASP Muhammad Jaligi, da aka rabawa manema labarai a Kaduna
Takardar ta bayyana cewa jami’an YAN Sanda ne masu aiki a ofishin yan sanda na Kakuri lokacin da suke aikin sintiri a kan baban titin Nnamdi Azikiwe a dai-dai Gadar Nasarawa da ke kan titin suka samu nasarar kama mutanen biyu.
Wadanda aka kama da zargin satar motar su hada da Abubakar Abdullahi da ke zaune a Unguwar Hayin Dan Mani sai kuma Gambo Musa da ke unguwar Rigasa a karamar hukumar Igabi cikin Jihar Kaduna.
An kuma samu nasarar samun wadansu motoci a wurinsu da suka hada da mota kirar Tayota Camry, mai launin uwan ganye dauke da lamba ABC 590 DX da kuma Mota kirar Tayota Corola mai launin ruwan Toka da lamba KTN 304 AG.
Takardar ta ci gaba da bayanin cewa a lokacin da ake yi wa barayin tambayoyi su da kansu suka ce suna cikin wani gungun masu kwacen motoci kuma a halin yanzu suna taimakawa Yan Sanda da muhimman bayanan da suke taimakawa a samu kamo sauran masu aikata laifin irin wanda aka same su da shi da niyyar kamasu baki daya.
Nasarar da ake samu a wannan runduna ta Kaduna na faruwa ne sakamakon irin Namijin kokarin da Kwamishinan Yan Sanda UM Muri ta fuskar aikin tattara sahihan bayanai da kuma aikin tsaro da nufin kawar da ayyukan batagari a Jihar. Don haka ne rundunar Yan Sandan Jihar Kaduna suke fadakar da daukacin jama’a da su bayar da gudunmawarsu a samar da nasarar da ake bukata.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.