Home / Garkuwa / Rundunar Yan Sanda Ta Kubutar Da Karin Mutane 20 A Kaduna

Rundunar Yan Sanda Ta Kubutar Da Karin Mutane 20 A Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin ganin ta kakkabe ayyukan batagari a cikin al’umma Rundunar yan Sanda ta kasa reshen Jihar Kaduna ta sanar da karin samun nasarar kubutar da mutane 20 daga hannun batagari da suka sace su a ranar 14 ha watan day 2020 a kan hanyar kaduna zuwa Zariya.
Rundunar ta dai bayyana sunayen mutanen kamar haka (1) Isa Sanni, (2) Shitu Azeez Olalekan, (3) Kadiri Nurudeen, (4) Raheem Rasheed, (5) Idris Yahaya, (6) Usman Abdullahi, (7) Isiyaku Jibrin, (8) Abubakar Mohammed, (9) Mu’azu Ibrahim
Sauran sun hada da  (10) Musa Alsami, (11) Haruna A. Ayuba, (12) Yau Sanusi, (13) Sunday Istifanus, (14) Thomas Joseph, (15) Olowoyeye A. Samuel, (16) Adamu Sani, (17) Usaini Haruna, (18) Sani Musa, (19) Ibrahim Hassan and (20) Adamu Ibrahim.
Guda biyu daga cikin wadanda aka sace din sun biya kudin fansa amma ba a sake su ba har sai da yan sandan suka kubutar da su tare da sauran Jama’ar da suke tare a hannun masu satar mutanen.
Bayanin hakan na kunshe a cikin takardar sanarwar da Rundunar ta fitar mai dauke da sa hannun jami’in da ke magana da yawunta DSP Yakubu Abubakar Sabo.
Inda takardar ta bayyana cewa nasarar ta biyo bayan irin yadda aka samu kubutar da wadansu Goma sha daya ne a ranar 21 da 22 ha watan Janairu 2020 a unguwar Mando da kuma yankin Kaduna zuwa Zariya
An kuma samu nasarar kubutar da wadansu mutane 9 a yankin Giwa da aka sace, an kuma yi wannan nasara ne lokacin da jami’an rundunar ke aikin neman batagarin, an kuma yi aikin ganin an dada su da yan uwansu.
Kwamishinan yan sandan na kaduna ya kuma yi kira ga daukacin al’umma da su ci gaba da taimakawa rundunar domin ganin an kakkabe batagari tare da ayyukansu baki daya.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.