Home / Labarai / Rusau: An Yaudare Mu Ne – Yan Kasuwar Unguwar Shanu

Rusau: An Yaudare Mu Ne – Yan Kasuwar Unguwar Shanu

Rusau: An Yaudare Mu Ne – Yan Kasuwar Unguwar Shanu

Mustapha Imrana Abdullahi

Wasu daga cikin yan kasuwar da ke neman abinci a cikin kasuwar unguwar Shanu Kaduna sun shaidawa manema labarai cewa su na zargin masu shugabanci a wannan kasuwa da yi masu shigo shigo ba zurfi har suka rushe rumfunan da suka gina tsawon shekaru masu yawa da suka gabata.

Yan kasuwar sun shaidawa tawagar manema labarai da suka ziyarci kasuwar domin sanin yadda lamarin ya faru.

A lokacin ziyarar manema labaran sun ga yan kasuwa manya da kanana su na Zanga zangar kokarin sai an cire masu wadanda ke yin shugabanci a kasuwar bisa zargin da suke yi masu cewa sun Yaudare su har suka rushe rumfunansu da kansu bisa dalilin cewa wai Gwamnati na bukatar samun wurin ajiye motoci a wurin da rumfunansu suke wasu tsawon shekaru kusan Arba’in da suka gabata.

“Tun lokacin da shugaba Buhari ke shugabanci a karkashin mulkin soja ya dauko kasuwar daga wurin da take tun farko ya dawo da ita kusa da babban ofishin ma’aikatar kula da Filaye ta Jihar Kaduna, kuma tun lokacin muke gudanar da kasuwanci a wurin wadansu ma sun Gaji rumfunan ne a kasuwar , amma sai yaudara ta shigo ciki a yanzu”, inji yan kasuwar.

Yan kasuwar musamman masu sana’ar sayar da kayan gwangwani a cikin kasuwar sun zargi wasu shugabanni a kasuwar da cewa sun kawo sunan su ne domin a raba kasuwar biyu a  tayar da su a bar dayan bangaren kasuwar.

Wakilinmu ya ga wata takardar taswirar zanen yadda kasuwar take da ita ma yan kasuwar suka yi zargin cewa akwai wanda ya zana biro da yan kasuwar suka yi zargin an raba kasuwar biyu ne tun daga bisani domin a rushe masu rumfuna a bangaren masu sana’ar Gwangwani a kasuwar.

Yan kasuwar ta Unguwar Shanu Kaduna bangaren masu sana’ar Gwangwani sun kuma yi Zanga zangar rashin amincewa da shugabannin kasuwar da Sarkin kasuwa bisa zargin da suke yi masu na yaudararsu har suka rushe rumfunansu da suke neman abinci a kasuwar su na samun abin da za su rufa wa kansu da iyalinsu asiri game da hidimar yau da kullum.

A nasu bangaren Khalid Usaini, Sarkin Kasuwar Unguwar Shanu Gundumar  kawo da Shugaban kasuwar Malam U  Dan Bawa cewa suka yi tun cikin watan Azumin da ya gabata ne suka samu wata takarda daga hukumar  KASUPDA cewa su na bukatar wani wuri daga cikin wannan kasuwar domin ma’aikatar kula da Filaye ta Jihar Kaduna na bukatar samun wurin ajiyar motoci a wani bangare a wannan kasuwa ta unguwar shanu.

Kamar yadda Sarkin kasuwar da shugaban suka shaidawa manema labarai cewa “lokacin da muka samu wannan takardar ne sai nan da nan muka je wurin hukumar da ke da alhakin aiko mana da takardar muka rakesu su bari har sai bayan Sallah, domin takardar da aka ba mu ta kowa ya bar kasuwar ne a cikin sati daya kuma cikin Sauri to, sai muka roka aka kuma amince, bayan da sakataren kungiyar kasuwa ya koma sai suka cewa mana ga wurin da suke bukata a cikin kasuwar da ke cikin geto”, inji Sarkin.

Da aka tambaye su ko an ba yan kasuwar wani wuri inda za su koma sai dukkansu Sarkin kasuwar da shugaban kasuwar suka amsa da cewa ba a ba su wani wuri ba, amma sun san kowa ne wuri har da inda suka gina gidajensu duk mallakin Gwamnati ne kuma za ta iya cewa ta na bukata a kowa ne lokaci.

Wannan shi ne Sarkin Kasuwar Unguwar Shanu gindumar Kawo Kaduna

Da wakilinmu ya tuntubi mai magana da yawun hukumar KASUPDA Nuhu Garba Dan Ayamaka, ya ce kokari yake ya samu shugabansa domin jin ta bakinsu game da lamarin a hukumace, don haka mu jira.

Don haka da mun samu jin ta bakinsu zaku ji bayani daga bangarensu Dalla dalla.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.