Home / Labarai / Sake Fasalin Naira: Mun Bi Tsarin Doka Da Tanajin Babban Bankin  Kasa Ne – Babban Bankin Najeriya

Sake Fasalin Naira: Mun Bi Tsarin Doka Da Tanajin Babban Bankin  Kasa Ne – Babban Bankin Najeriya

 

 

 

Bayanan da ke fitowa daga babban birnin tarayyar Najeriya ABUJA na cewa, sabanin irin yadda ministar kudi, kasafin kudi da tsare – tsare, Zainab Ahmad, ta ce wai ba su da masaniyar cewa babban Bankin Najeriya (CBN) sai sake Fasalin takardun kudin Kasar guda uku, amma babban Bankin ya ta bayar wa da duniya cewa sun bi duk tsarin doka da tanaje tanajen da ke kunshe cikin tsarin tafiyar da Bankin, domin aiwatar da tsarin da ya dade ba a yi ba tun tsawon shekaru sha biyu (12).

 

 

Da yake magana da gungun wadansu manema labarai a Daren jiya Juma’a a Abuja, mai magana da yawun babban  Bankin Mista Osita Nwanisobi, ya bayyana mamakinsa ne da irin kalaman ministar kudi, inda ya ce babban Bankin Najeriya ya kasance wani wurin da ake aiwatar da komai a bisa tsarin bin doka da oda a dukkan abubuwan da yake tafiyarwa ko gudanarwa.

 

Kamar yadda Nwanisobi, ya ce manyan Jagororin da suke tafiyar da babban Bankin Najeriya bisa tanajin dokar sashi na 2(b), sashi na 18(a), da kuma sashi na 19(a)(b) na tsarin dokar Babban Bankin Najeriya na shekarar 2007, inda ta ce daga zaran an samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari idan an rubuta masa game da batun sake Fasalin takardar naira da Bankin ya fitar kuma suke zagaya wa a hannun jama’a a dukkan wurin hada hadar kudi, musamman takardun dari 200, dari Biyar da dubu daya 1,000 na takardun kudin.

 

Sai ya shawarci yan Najeriya da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga wannan aikin sake Fasalin takardun kudin, da ya ce ana yinsa ne domin kare martaba da mutunci tare da ci gaban kowa ne dan kasa, sai ya kara da cewa akwai wadansu mutane da suka boye wadansu takardun kudi ba tare da kai su bankunan kasuwanci ba. Saboda haka ba za a karfafa wa irin wannan tsarin Gwiwa ba musamman ga duk mai fatan alkairi ga kasa.

 

Ya kara da cewa, batun tafiyar da  takardun kudin kasa ya sha fama da kalubale iri – iri, wanda hakan na shafar batun darajar kudin  kasar, Don haka Babban Bankin kasa da kuma kasar sun tashi tsaye wajen kare martaba da darajar kudin takardar naira, a wadatar da kasar da takardun kudin da kuma tsare dukkan sharuddan da ke tattare da hidimar kudi.

 

A game da batun sake Fasalin takardun kudin,Nwanisobi sai ya yi bayanin cewa, babban Bankin ya yi Namijin kokari kwarai domin kuwa ya kasance har tsawon shekaru 20 kafin ya gudanar da wannan aikin na sake Fasalin takardar naira, duk da cewa irin yadda yadace ayi wanda kuma shi ne ake gudanarwa a duk fadin duniya shi ne ana aiwatar da sake Fasalin kudin ne da kuma shigar da su ga jama’a a kowane shekaru biyar zuwa Takwas.

 

Ya baya yan Najeriya tabbacin cewa wannan aikin sake Fasalin kudin aiki ne na Babban Bankin kasa, don haka ba wai ana kokarin yi bane saboda wani ko wasu mutane ba, mai magana da yawun bank8n ya bayyana cewa hakan zai taimakawa kokarin da ake na yin hada hadar kudi ta hanyar amfani da intranet ya kuma kara kaimin aikin da ake yi na eNaira.

 

Kuma hakan zai taimaka wajen maganin yan Ta’adda da masu satar mutane domin irin yadda ake amfani da makudan kudi ba tare da amfani da Bankuna ba domin ana biyan makudan kudin fansa bayan an sace mutane.

 

 

 

Sai Nwanisobi, ya shawarci yan Najeriya, a ko’ina suke, da su ci gaba da bayar da hadin kai da goyon baya da wannan aikin sake Fasalin Naira, domin samun ciyar da tattalin arzikin kasa gaba.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.