Home / Ilimi / SAKON MAULUD DAGA KHADIMUL ISLAM, GWAMNA BALA MUHAMMAD ABDULKADIR NA JIHAR BAUCHI.

SAKON MAULUD DAGA KHADIMUL ISLAM, GWAMNA BALA MUHAMMAD ABDULKADIR NA JIHAR BAUCHI.

 

A RANA IRIN TA WANNNAN LOKACI 2021 MUNA TAYA DAUKACIN AL’UMMAR MUSULMAI MURNAR ZAGAYOWAR HAUHAWAR FIYAYYEN HALITTA (SAW) WADDA YAZO A RANAR TALATA 19|10|2021 (11|RABI’UL AWWAL 1443)

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai, mamallakin duniya, Yadda da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad SAW da Iyalan Gidansa.

Al’ummar jihar Bauchi, mukara Gode wa Allah da yasake bamu wannnan damar na sake ganin Wannan Shekara na Murnan zagayowar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) Allah yakara yadda dashi wadda yazo da yada Addinin Allah a duniya, wadda yakawo Sauyi da hadin’kai a tsakanin al’umma, bayan Wannan shi yazo da wahayi wadda yayada bishara wa al’umma na koyar da Gaskiya, rikon amana, hakuri, Son juna, da kuma tsoron Allah.

Wadannan duk yakawosu yakoyar dasu batare da nuna banbancin Addini ba yakuma sasu suka zamo a aikace.

2 – Kamar yadda Muke Murnan zagayowar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

ina kara Kira da muyi koyi da halayensa dakuma dubi da abunda da kowa yayi baya don bincikan Kawunammu da alakar mu da Allah a Shekarar data Wuce don samun aihin chanji kan laifuka don Ayi gyara.

Adai dai wannan Lokaci, Ina bukatar al’ummar Musulmi dasuyi addu’oi na zaman lafiya, Ina kuma kara Kira ga al’ummar jihar Bauchi da su zauna lafiya da son juna a tsakani batare da nuna banbancin Addini ko yare ba, Kowa yayi addu’oi wa jihar da kasa baki daya kan tabarbarewar tsaro da ya Addabi wasu sassa na kasannan.

3 – Bari inyi anfani da wannan Lokaci in kara tabbatar wa al’ummar da irin kokari da karfin gwiwa na Gwamanti wajen ganin an tabbatar da bin doka da Oda, Gwamanti ta hada kai da hukumomin tsaro, na daukar aihin matakai na ganin an tsare lafiya da dukiyoyin al’umma a jihar.

Ina kuma kara neman goyon Bayanku wajen bada hadin’kai wa Gwamanti don a cigaba da samun zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Gwamanti bazata zuba wa wasu dasuke son kawo tarzoma da karya doka ido ba, Duk wadda aka samu da hanu cikin aikata laifi Gwamanti zata hukuntasu dai-dai da doka.

 

4 – Akarshe, Ina tayamu Murnan zagayowar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW, Ina kuma addu’an Allah yasa Ayi bukukuwan Mauludi lafiya batare da Wani tangarda ba.

Allah yakara bamu zaman lafiya albarakacin Annabi Muhammad SAW yacigaba da taimakon mu yakare mu baki daya.

 

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.