Home / Labarai / Sallar Idi: A Yi Wa Buhari Da El- Rufa’i Addu’ar Samun Nasarar Kalubalen Tsaro – Sardaunan Badarawa

Sallar Idi: A Yi Wa Buhari Da El- Rufa’i Addu’ar Samun Nasarar Kalubalen Tsaro – Sardaunan Badarawa

Daga Wakilin Mu

YAYIN da al’ummar Musulman duniya ke sake gudanar da wani bikin babbar Sallar Layya (Idi-El-Kabir) don tunawa da sadaukarwa da biyayya ga umarnin Allah da Annabi Ibraham da dansa Ismail, tsohon shugaban rikon karamar hukumar  Kaduna ta Arewa Honarabul Usman Ibrahim, wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa ya roki addu’o’i daga wajen musulmai masu aminci ga shugaba Buhari da Gwamna Nasiru El-Rufa’i don shawo kan matsalolin tsaro a Jihar Kaduna da Najeriya baki daya.

Honarabul Ibrahim a sakon da ya aike domin taya al’umma murnar babbar Sallah, ya bayyana kwarin gwiwarsa bisa ga irin nasarorin da Gwamna Malam Nasiru El-Rufai ya samu da daukaka duk da kalubalen tsaro da ke addabar jihar wanda ya lura nan ba da dadewa ba zai zama tarihi saboda a cewarsa gwamnan ba zai bar wata kafa ba wajen dawo da dawwamammen zaman lafiya zuwa babban cibiyar yankin Arewa.

 

 

Ya kara da nanata karfin ikon yin addu’o’i, musamman na mutanen da ke cikin wani halin kunci, inda ya bayyana cewa tabbas Allah zai amsa addu’o’in duk wasu Musulmai ga shugabannin su a daidai lokacin bikin Sallah.

 

 

Dan takarar Sanatan Kaduna ta Tsakiya a shekarar 2019 wanda kuma ke rike da sarautar gargajiya ta San-Turakin Hausa, ya danganta kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta ga halaye marasa kyau na ‘yan Najeriya da neman daukin Allah a cikin lamuran su, yana mai jaddada matsayin da ya kamata wajen yin addu’o’in cimma babban rabo.”

 

 

“Ba ni da wata shakku game da irin sahihancin shugabanninmu a matakin jihohi da tarayya don samar da kyakkyawan jagoranci na kwarai wanda zai iya sauya rayuwar al’umma ta hanyar da ta dace.”

 

 

“Wannan yana iya zama shaida ga ci gaban abubuwan ci gaban yau da kullum da ake samu a duk fadin Najeriya don sauya labarai da tasirinsu musamman game da rayuwar mazauna karkara da mata.”

 

 

“Tsarin layin dogo da aka sabunta tare da zamanantar da shi domin saukaka safarar mutane da kayayyaki a duk fadin kasar yana nuni ne kan cewa lokaci ya yi da za a samu kyakkyawar nasara.”

 

 

“Jihar Kaduna, babban birnin ce ta musamman da Gwamna El-Rufai ya ba ta kulawa wanda kusan ya canza komai game da hangen nesan garin ta hanyoyin sabunta birane.”

 

 

“Ina kira ga mutanen kirki na yankin Kaduna ta Tsakiya da su yi amfani da wannan lokacin sallah don yin addu’ar zaman lafiya, jituwa da ci gaban jihar baki daya.”

 

 

“Ci gaban zai iya bunkasa ne kawai ta hanyar yin hakan sannan kuma a same shi a cikin yanayi na alkawuran juna inda ‘yan ƙasa ke ganin nasara da gazawar shugabanninsu kamar nasu, “in ji shi.

 

 

Ya kuma yi kira ga masu sayar da kayan abinci da masu sayar da Raguna da su saukakawa jama’a ta yadda farashin zai zama abin da kowa zai iya samun yin layya da sukunin shagulgulan Sallah cikin walwala da jin dadi.

 

 

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.