Home / Labarai / Samar Da Tsaro Sai Kowa Ya Bayar Da Gudunmawarsa – Kaftin Joji

Samar Da Tsaro Sai Kowa Ya Bayar Da Gudunmawarsa – Kaftin Joji

….A koma ga masu unguwanni, dagatai da hakimai

Kaftin Muhammad Joji ya bayyana cewa lallai ya dace kowa ya a tashi tsaye a hada kai kowa ya bayar da gudunmawarsa domin a samu ingantaccen tsaro a kasa baki daya

Kaftin Muhammad Joji, ne ya yi wannan kiran lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.

Joji ya ci gaba da bayanin cewa aikin tsaro wani lamari ne na kowa da kowa domin ba aikin mutum daya ba ne.

” Tun daga kan Dagatai hakimai da masu unguwanni duk aikin kula da tsaro ya shafe su baki daya, a daina zuwa haka kawai ana ta kashe wadansu kudade ba gaira ba dalili, a kira Dagatai da masu unguwanni za’ a samu warware matsalar tsaron. Amma idan an yi watsi da su sai kowa ya rike hannayensa ya koma gefe kawai. Don haka yakamata a sake dawowa da mutanen nan a duba Dagatai, hakimai da masu unguwanni a tara su a gaya masu cewa duk abin da ya faru a yankin unguwarsa kai za a yi wa magana don haka me za mu yi maka kowa ya fadi abin da za a yi masa na taimako domin kada wani abu na matsalar tsaro ya faru. Ina tabbatar maku cewa harkar tsaro za ta gyaru kwarai, saboda a da can mutum zai ta fi da kafarsa tun daga Kaduna har Abuja da kafa ba wani abin da zai faru ba tsoro ba komai, amma yanzu fa daga nan zuwa nan ma lamarin ya zama sai addu’a ta yaya kai da kasarka za a ce ba zaka iya tafiya daga nan zuwa can ba? ai hakan ba dai- dai ba ne don haka yakamata a hada kai a tashi tsaye kowa ya bayar da tasa gudunmawar a samu warware matsalar tsaro domin ba aikin mutum data ba ne.

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.