Home / News / Sarkin Zazzau Na 19 Nada Kyakkyawan Nufi, Tunani Ga Masarautar Zazzau

Sarkin Zazzau Na 19 Nada Kyakkyawan Nufi, Tunani Ga Masarautar Zazzau

Sarkin Zazzau Na 19 Nada Kyakkyawan Nufi, Tunani Ga Masarautar Zazzau

Mustapha Imrana Abdullahi

Dan Majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Karamar hukumar Zariya Honarabul Dokta Abbas Tajuddeen (T J) ya bayyana sabon mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli da cewa mutum ne mai kyakkyawar manufa ga masarautar Zazzau da al’ummarta baki daya.

 

Honarabul Abbas Tajuddeen ya ce hakika idan mutum ya ji irin kalaman mai martaba Sarkin Zazzau na 19 da ya yi a wajen karbar Sanda da kuma rantsuwar kama aiki hakika ya san akwai manufa mai kyau da zai yi wa masarautar aikin ci gaba.

 

Dokta Abbas Tajusdeen ya bayyana hakan me jim kadan bayan ya saurari jawabin mai martaba Sarkin Zazzau a filin kwallon Dawaki da ke Zariya.

 

 

Dokta Abbas ya ci gaba da cewa shi a matsayinsa na wakilin jama’a yana kira ga daukacin al’umma a ko’ina suke su bayar da hadin kai da goyon baya ga Mai martaba Sarkin Zazzau domin ya samu sukunin yi wa jama’a aiki.

 

 

Ga wadanda suka nemi sarautar ba su samu ba to, su dauki hakuri da Tauhidi tare da bayar da hadin kai da goyon baya ga Mai martaba Sarkin Zazzau domin Allah ne ke bayarwa, a kuma yo masa fatan alkairi yasa hakan shi ne mafi alkairi ga kowa.

 

 

Ya kuma kara da fadakar da cewa a batun Zanga zangar neman ci gaban matasa da a tun farko aka yi a kwanan baya a tarayyar Nijeriya, honarabul Dokta Abbas cewa ya yi hakika a farko sun yi zaton neman ci gaba ne amma sai daga baya aka ga lamarin ya dauki wani sabon Salo na daban “mun ji dadi kwarai da matasan arewa suka fahimci abin da aka yi nufi da Zanga zangar kuma suka kiyaye daga shiga cikinsa, wannan hakika an samu nasara kwarai don haka muna yi wa matasan Arewa godiya”.

 

Dan majalisar ya kuma kara da fadakarwa game da abin da ke haifar da tashin tashina inda ya ce abin da ke haifar da su abubuwa biyu ne na farko rashin cikakken ilimi da rashin abin yi, saboda haka idan Gwamnatinza ta tsaya tsayin daka ta tabbatar da wadannan abubuwa biyu su tabbata an magancensu to ko an yi irin wannan rikicin ba inda za shi.

 

 

“Wannan alamu ne da ke cewa kasarnan na neman canje canje a wajen salon shugabanci da yadda ake tafiyar da tattalin arzikin kasa wanda ba za a ce yanzu ne matsalar ta fara ba domin abu ne mai Dogon tarihi, matsalar ta dade ana fama da ita saboda haka ba lokaci guda ne za a iya cewa Gwamnati kawai za ta kawo karshen sa ba, abune da Bature me cewa ana fadakar da kowa ga duk wani da ya kasance shugaba a kasarnan, in bamu dauki hanyoyin gyara na inganta rayuwar matasa to yakamata a Sani inganta rayuwar matasa ne babban al’amari domin ya dace a sani muna kan babban Bom ne kuma ranar da ya tashi Allah kadai ya san ta’adin da zai yi, don haka Allah ya kare mu

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.