Home / Labarai / Sarkin Zazzau Ya Nada Abdullahi Kwarbai Jami’in Hulda Da Yan Jarida

Sarkin Zazzau Ya Nada Abdullahi Kwarbai Jami’in Hulda Da Yan Jarida

Mustapha Imrana Andullahi

 

Mai martaba Sarkin Zazzau Jakada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya nada Abdullahi Aliyu Kwarbai, tsohon ma’aikacin kamfanin wallafa jaridu na New Nigeria a matsayin jami’in hulda da yan jarida da kuma yada bayanai.

Takardar nadin ta bayyana cewa nadin ya fara aiki ne tin ranar 12 ga watan Yuni, na shekarar 2021 da ke dauke da sa hannun mataimakin sakataren masarautar, Alhaji Umar Shehu Idris, Dan Isan Zazzau, inda ya bayyana cewa nadin za ayi aiki ne bisa tsarin aikin kwantaragi.

Kafin nadin nasa Abdullahi Aliyu Kwarbai ya yi aiki ne a kamfanin wallafa jaridun New Nigeria da Gaskiya Ta Fi Kwabo daga shekarar 1985 zuwa 2006 a matakai daban daban, da ya hada da mai’aikin sarrafa na’ura mai kwakwalwa a bangaren aikin jarida kafin nan ya koma bangaren neman tallace tallace na kamfanin a matsayin manaja mai kula da dukkan shiyyar Arewa maso Gabas a Bauchi har zuwa lokacin ajiye aikinsa a shekarar 2006.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.