Home / Labarai / SHEIKH El – ZAZZAKY YA TAIMAKAWA YAN JARIDA DA ABINCIN AZUMI

SHEIKH El – ZAZZAKY YA TAIMAKAWA YAN JARIDA DA ABINCIN AZUMI

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
SAHARARREN Malamin addinin musulunci da ke tarayyar Najeriya Sheikh Ibrahim Yakubu El- zazzaky ya taimakawa yan jarida da abincin Azumi.
Da yake mikawa manema labaran a Jihar Kaduna kayan abincin Azumin Malamin addinin Kirista Fasto Yohanna Y. D Buru, ya shaidawa yan jaridar cewa Malam Sheikh Ibrahim Yakubu El – zazzaky ne ya bashi wannan kayan abincin Azumi domin ya mikawa yan jarida ta yadda suma za su samu damar yin walwala tare da farin ciki da iyalansu a watan Azumin Ramadana da ake ciki. “Kuma hakan zai taimaka wajen samun zaman lafiya da walwalar rayuwar jama’a don haka Malam Zazzaky ya aiko da wannan kayan abincin a ba yan jarida”.
“Ko a jiya da Sheikh Ibrahim Yakubu El- Zazzaky ya bayar da kayan abinci aba matan da mazajensu suka rasu ga marayu su na tare da su a yankin Kudancin Kaduna, irin yadda labaran da yan jarida suka bayar hakika jama’a da dama duk sun yi murna da farin ciki da samun labarin taimakon da aka ba dimbin jama’a, ya bayyana wa manema labaran cewa bisa irin kokarin da yan jarida ke yi ne ya sa a halin yanzu Malam Zazzaky da kansa ya ce in kawo maku wannan kayan abincin da suka hada da Shinkafa, Masara, Dawa da Gero domin kowa ya samu sukunin yin walwala tare da iyalansa”. Inji Fasto Buru.
Ya ci gaba da cewa hakika Malam Sheikh Ibrahim Yakubu El- Zazzaky ya na godiya da irin kokarin da kuke yi. Kuma kamar yadda kuke ganin wannan kayan abincin naku haka aka aika da shi zuwa wadansu Jihohin a cikin kasar nan da nufin sama wa jama’a saukin rayuwa.
Kuma hakan zai taimaka wajen tabbatar da samun zaman lafiya da ciyar da al’umma gaba.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.