Home / Big News / Shirin Ceto Zamfara Na Samun Nasara, Yayin Da Gwamna Lawal Ke Duba Ayyuka A Shinkafi

Shirin Ceto Zamfara Na Samun Nasara, Yayin Da Gwamna Lawal Ke Duba Ayyuka A Shinkafi

 

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa shirin ceto jihar sa daga halin da take ciki, wato “Rescue Mission” yana tafiya yadda ya dace kuma yana haifar da gagarumin sakamako.

A ranar Laraba, gwamnan ya kai ziyarar aiki a Ƙaramar Hukumar Shinkafi domin duba manyan ayyukan da gwamnatin jihar sa ke aiwatarwa a yankin.

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa a lokacin ziyarar, Gwamna Lawal ya halarci bikin ƙaddamar da shirin tallafawa al’umma da ɗan majalisa mai wakiltar Shinkafi/Zurmi a Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Bello Hassan Shinkafi, ya shirya.

Shirin tallafin ya amfanar da mutane 2,000 ta hanyar raba motoci masu kyau, kekunan hawa, babura, injinan ɗinki da sauran kayan taimako.

A cikin wannan ziyara, Gwamna Lawal ya duba Cibiyar Kula da Mata da Yara (WCWC) a garin Shinkafi, wadda aka bayar domin cikakken gyara. Haka kuma, ya ziyarci Babban Asibitin na Shinkafi wanda aka gyara tare da sabunta kayan aikin sa, da kuma sabon asibitin gaggawa ‘Referral Hospital’ da ke nan a cikin garin.

A fadar Sarkin Shinkafi, Gwamna Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na aiwatar da manyan ayyuka a dukkan ƙananan hukumomin jihar.

Ya ce, “Mun zo Shinkafi yau domin duba muhimman ayyukan da gwamnatin mu ke gudanarwa tare da ƙaddamar da shirin tallafin ɗan majalisar tarayya, Hon. Bello Hassan Shinkafi.

“Mun kammala gyaran babban asibitin Shinkafi tare da samar masa da na’urori na zamani da za su taimaka wajen kula da lafiya cikin gaggawa ga al’umma.

“Sabon asibitin gaggawa zai zama jigo wajen inganta kiwon lafiya, ba kawai a Shinkafi ba, har ma ga dukan yankin arewacin Zamfara. Wannan zai rage wa jama’a wahalar neman kulawar likitoci.”

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta mallaki tsohuwar makarantar Bafarawa domin mayar da ita Cibiyar Karatun Kimiyyar Lafiya ta Jami’ar Jihar Zamfara, inda ake ci gaba da aikin gyara don fara amfani da ita nan ba da jimawa ba.

Gwamna Lawal ya yaba wa Hon. Bello Hassan bisa irin wannan shirin taimakon al’umma, tare da kira ga sauran shugabanni da su mayar da hankali kan ci gaban ɗan adam.

SULAIMAN BALA IDRIS
Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara
7 ga Janairu, 2026

About andiya

Check Also

Jam’iyyar ADC Na Samun Gagarumar Nasara A Zamfara – Bashir Nafaru

  Daga Imrana Abdullahi  Honarabul Bashir Nafaru, Sakataren Kudi na jam’iyyar ADC jihar Zamfara,ya bayyana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.