Home / News / Shirin WYEP Domin Inganta Rayuwar Matasa Ya Yi Wa Mutane 484 Rajista A Kaduna

Shirin WYEP Domin Inganta Rayuwar Matasa Ya Yi Wa Mutane 484 Rajista A Kaduna

Shirin WYEP Domin Inganta Rayuwar Matasa Ya Yi Wa Mutane 484 Rajista A Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi

Shirin inganta harkokin Noma na Bankin duniya da ake kira ( APPEALS) da ke kokarin inganta Mata da Matasa ( WYEP) a Jihar Kaduna ya yi wa mutane dari 484 rajista da hukumar yi wa kamfanoni da masana’antu ta kasa, (CAC).

Wani da ake yi wa lakabi da sunan mai mata da matasa Ibrahim Yakubu Yakubu wajen babban taron bayani a kan nasarorin da aka samu karkashin shirin WYEP a Jihar Kaduna cewa sun yi kokarin aikin lalubo wadanda za a horar a kan yadda ake tsara hanyoyin kasuwanci domin su amfana.

Ibrahim Yakubu ya ce shirin WYEP wani bangare ne na APPEALS wanda shiri ne na babban Bankin duniya da ake saran mutane 1,700 za su amfana.

Ya ci gaba da cewa kashi 50 na wadanda suka amfana a karkashin shirin mata ne.

 

Yakubu ya tabbatar da cewa abubuwan da ake yi karkashin shirin sun hada da Noman Masara, samar da Nono, Noman Shinkafa, Alkama,Kashu, Jinja da sauransu.

Babbar manufar yin hakan ita ce a kara fadakar da jama’a game da harkokin Noma.

“Yadda muka dauko wadanda suka amfana da wannan shirin ya fara ne daga fadakar da mutane daga baki dayan kananan hukumomi 23 da ke Jihar Kaduna a shekarar 2019.

Masanin harkar ya ci gaba da cewa sai da aka Sanya talla a manyan jaridun daily trust da blueprint da kuma kafafen rediyo da dandalin Sada zumunta.

An dai zabo wadanda suka amfana din ne ta hanyar bin tsarin gaskiya da adalci.

REPORT THIS YA KARA DA CEWA AN BAYAR DA TAKARDU GA WADANDA SUKA AMFANA MUTANE DUBU 1,700 A WATAN DISAMBA, 2019.

Ya kara da cewa wadanda suka amfana an horar da su ne daga cibiyoyi guda uku, yayin da wadanda kuma ana saran a horar da su sakamakon matsalar da aka samu a lokacin cutar Korona sai aka Dakatar da tsarin amma za a ci gaba da yinsa a cikin watan Nuwamba a wannan shekarar.

Ya ce batun shirye shiryen tsaya kasuwanci an yi shi ne a dukkan bangarorin Jihar na yankin Zariya,Kafanchan da Kaduna.

 

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.